Ashafa Murnai Barkiya
Aƙalla kashi 65 bisa 100, wato fiye da rabin ’yan Nijeriya da aka tambaya a wani bincike da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gudanar a baya-bayan nan, sun nuna cewa suna son a rage kuɗin ruwa kan rance da lamunin da bankunan kasuwanci ke bayarwa ga masu masana’antu da kamfanoni da ‘yan kasuwa.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin taron Kwamitin Tsare-tsaren Manufofin Kuɗi na CBN da za a gudanar cikin mako mai zuwa.
Masu neman a yi rangwamen dai suna ganin hakan zai amfani tattalin arziki, kamar yadda kowanen su ya nuna daban-daban.
“Yawancin masu amsa tambayoyin sun fi son a rage kuɗin ruwa, inda kashi 65.0 cikin 100 suka nuna buƙatar a sauƙaƙa kuɗin ruwan”, kamar yadda CBN ya bayyana a Sabon Binciken Hasashen Manufofin Tattalin Arziki.
Binciken ya ƙara ƙarfafa hasashe kan alƙiblar Ma’aunin Kuɗin Ruwa na Manufofin Tsare-tsaren Kuɗi (MPR) yayin da masu tsara manufofi ke shirin ganawa a ranakun 25 da 26 ga Fabrairu, a daidai lokacin da matsin farashi ke raguwa, kuma naira ke ƙara samun daidaito da kuma tagomashi a kasuwar musayar kuɗi.
Duk da damuwar da ke cewa rage kuɗin ruwa na iya kawo cikas ga yaƙi da hauhawar farashi, kashi 50.1 cikin 100 na masu amsa tambayoyin sun fi son a rage kuɗin ruwa, lamarin da ke nuna irin tasirin tsadar kuɗin ga gidaje da kasuwanci.
Nijeriya ta ci gaba da bin tsauraran manufofin kuɗi, matakin da ya taimaka wajen daƙile hauhawar farashi bayan ya kai matakin da ba a gani kusan shekaru talatin ba a 2024.
Sabbin alƙaluma daga Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewa hauhawar farashi ya sauka kaɗan zuwa kashi 15.10 cikin 100 a watan Janairu, daga kashi 15.15 cikin 100 a Disamba 2025.
Naira ma na nuna alamun daidaito, inda aka nuna farashin ta a N1,355.42 kan dala a farashin hukuma, a ranar 13 ga Fabrairu, idan aka kwatanta da sama da N1,400 a farkon shekara.
Waɗannan sauye-sauye na iya bai wa masu tsara manufofin kuɗi damar duba yiwuwar sassauta manufofi bayan rage kuɗin ruwa na farko cikin shekaru biyar da aka yi a Satumba 2025, lokacin da aka daidaita shi zuwa kashi 27 cikin 100.
Binciken ya kuma nuna ra’ayoyi mabambanta game da yanayin tattalin arziki. Ma’aunin dai ya tsaya a maki 2.8 a Janairu 2026, daga maki 4.8 a Disamba 2025. Duk da ragin da aka samu a wata-wata, sakamakon na nuna wata na uku a jere na kyakkyawan fata kan bunƙasar tattalin arziki.
Ma’aunin yanayin tattalin arziki ya kai maki 7.4, wanda ke nuna cewa masu amsa tambayoyin na ganin akwai daidaito ko ingantawa a manyan alamu na tattalin arziki.
Sai dai ra’ayi kan halin kuɗi da samu na iyalai ya ci gaba da zama mara ƙarfi. Ma’aunin halin kuɗi na iyali ya tsaya a maki -8.2, yana nuna cewa gidaje da dama na fuskantar ƙalubale.
Wannan bambanci tsakanin yadda jama’a ke kallon tattalin arzikin ƙasa da halin da suke ciki na ƙashin kai na nuna matsin da iyalai ke fuskanta duk da ingantuwar wasu manyan alamu.
Tsadar kuɗin ruwa na ƙara nauyin biyan basussuka, yayin da sharuɗɗan bada bashi ke ci gaba da tsauri.
Hukuncin da Kwamitin Manufofin Kuɗi zai yanke na gaba zai zama gwaji ga manufar CBN wajen fifita yaƙi da hauhawar farashi a daidai lokacin da ake fuskantar matsin tattalin arziki.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya sha nanata goyon bayan sa ga tsauraran manufofi domin daidaita hasashe da kare ƙima da amincin manufofi. Amma tsadar kuɗin ruwa ya kuma ƙara tsaurara sharuɗɗan bashi, tare da dagula wa masana’antu, ƙananan ’yan kasuwa, da masu amfani.
Sakamakon binciken CBN ya nuna cewa buƙatar rage kuɗin ruwa na da ƙarfi, yana kuma haskaka matsin da ake fuskanta a matakin jama’a, inda gidaje da kamfanoni ke fama da raunin ƙarfin saye da tsadar kuɗin.
Saboda haka, taron MPC na Fabrairu zai fi zama abin lura ba kawai kan hasashen hauhawar farashi ba. Tsayawa kan yadda ake yanzu zai nuna ci gaba da mayar da hankali kan daidaiton farashi da amincewar masu zuba jari. Rage kuɗin ruwa kuwa zai nuna sauyin akala zuwa tallafa wa buƙatar cikin gida da rage tsadar samun kuɗi.
