Borno Ta Fi Kowace Jiha Juriya a Nijeriya – Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Borno a matsayin jihar da ta fi kowace jiha juriya a Nijeriya, domin mutanen ta sun ƙware wajen shawo kan duk wani ƙalubale.

Idris ya bayyana hakan ne a Maiduguri a ranar Laraba, yayin da ya kai ziyarar ban-girma ga Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a cikin jerin ayyukan da ke gudana a Taron Kwamishinonin Yaɗa Labarai na APC.

Ya ce: “Jihar Borno ita ce jihar da ta fi kowace jiha juriya a Nijeriya, idan aka yi la’akari da ƙalubalen da ta fuskanta a cikin shekaru goma da suka gabata.”

Ministan ya ƙara da cewa ya kamata duk ‘yan Nijeriya su yaba wa mutanen Borno bisa jajircewar su da kuma yadda suke farfaɗowa duk lokacin da suka shiga mawuyacin hali.

“Mutanen Jihar Borno suna nuna ƙarfin hali da juriyar da ‘yan Nijeriya ke da shi gabaɗaya, kuma ya dace sauran ‘yan ƙasa su yaba musu ba kawai da kalmomi ba, har ma da alfahari da yadda suke iya shawo kan ƙalubale,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *