Gwamna Lawal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gwamnan Shekara Ta Jaridar LEADERSHIP, Ya Sake Jaddada Ƙudirin Ci Gaban Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na kawo sauyi mai ma’ana da farfaɗo da ƙwarin gwiwar al’umma ga harkokin mulki a jihar. Gwamnan ya karbi Kyautar “Gwarzon Gwamnan Shekara” ta jaridar LEADERSHIP a ranar Alhamis, yayin taron shekara-shekara na jaridar da aka gudanar a Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa…

Read More

Tinubu ya naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa, ya kuma sabunta shugabancin NEMSA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hon. Magaji Da’u Aliyu a matsayin Darakta Janar (MD) na Sheda Science and Technology Complex (SHESTCO), Abuja, cibiyar da ke da alhakin bincike da bunƙasa fasaha tare da kula da cibiyar binciken nukiliya ta ƙasa. Haka kuma, shugaban ƙasar ya naɗa Injiniya Adesayo Olusegun Michael a…

Read More

TARON NEC NA 2026: Gwamnan CBN ya yi gargaɗin barazanar yawan kuɗi da guguwar zaɓen 2027 kan nasarorin tattalin arziki da aka sha wahalar samu

Ashafa Murnai Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi gargaɗi cewa yawan kuɗin da ke danfare a cikin tsarin kuɗi da kuma shigowar zagayen zaɓen shekarar 2027 na iya zama babbar barazana ga kwanciyar hankali da tattalin arzikin ƙasar ya samu kwanan nan. Cardoso ya buƙaci a kula sosai domin kare gyare-gyaren da…

Read More

Shettima ya jajanta wa al’ummar Kaiama, ya tabbatar da ƙudirin Shugaba Tinubu na dawo da zaman lafiya a Faɗin ƙasar.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci wata tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara domin jajanta wa al’ummar yankin da Gwamnan Jihar, Mallam AbdulRahman AbdulRazaq, bisa mummunan harin ta’addanci da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama. Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar damuwa a ƙauyukan…

Read More