Ashafa Murnai
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata wani bauɗaɗɗen rahoton da aka ce ya sayar wa manyan dillalan mai har Dalar Amurka biliyan 1.259, domin su shigo da fetur da dangogin sa daga waje.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai ta CBN, kuma Daraktar Riƙo ta Hulɗa da Jama’a, Hakama Sidi Ali ta fitar, ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, ba a yaɗa gaskiyar yadda lamarin yake ba.
“Kuɗaɗen waɗanda adadin su ya kai Dala biliyan 1.259, waɗanda aka buga cikin jadawalin bayanan Adadin Musayar Kuɗaɗe na Watanni Ukun Farko na Shekarar 2025, suna nufin adadin kuɗaɗen da aka yi musaya a tsarin musayar kuɗaɗe na NFEM a fannoni daban-daban, har da fannin fetur da gas. Kuma a bisa cinikin da ya gudana can a tsakanin masu sayar da kuɗaɗe da masu saye, ba a CBN ba.”
Hakama ta ce tun bayan da aka haɗe tsarin musayar kuɗaɗen waje wuri ɗaya a ƙarƙashin NFEM cikin 2023, ‘yan kasuwa ne da kan su ke samo kuɗaɗen canji, ba CBN ke sayar masu ba.
Don haka ta ce “musamman ma batun sayar wa masu shigo da fetur Dalar Amurka, ko masu shigo kowane kaya, duk CBN bai sayar masu da Dala ba.”
Ta ce adadin wanda aka ci karo da shi a jadawalin, yana nufin adadin yawan Dalar da ‘yan kasuwa suka sayar wa masu sayen kuɗaɗen waje bisa tsarin da CBN ya gindaya, a cikin watanni ukun farkon watan Oktoba, 2025, wato Q1 2025.
