CBN ya ɗaga darajar Opay, Moniepoint da su Palmpay zuwa cikakkun bankunan ƙasa baki ɗaya

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗaga matsayin darajar lasisin wasu manyan kamfanonin fasahar kuɗi (FinTech) da ƙananan ‘microfinance’, ciki har da Opay da Moniepoint, zuwa lasisin ƙasa (national license).

Hakan ya biyo bayan cika dukkan sharuɗɗan da CBN ɗin ya gindaya masu, wanda ke ba su damar gudanar da ayyukan su a duk faɗin ƙasar. An ɗaga likkafar su bayan sun cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada.

Sabon tsarin ya shafi manyan kamfanoni kamar Moniepoint Microfinance Bank, Opay, Kuda Bank, Palmpay da Paga, waɗanda suka bunƙasa cikin sauri ta hanyar amfani da fasahar wayar hannu da hanyoyin wakilan ejan-ejan bisa turbar hadahadar kuɗaɗe ta zamani (agent networks).

Wannan ci gaban hadahadar zamani ta haifar masu saurin cika sharuɗɗan tsallake matsayin su na masu hadahada a taƙaitattun yankuna, inda a yanzu suka zama masu cikakkun lasin ƙasa baki ɗaya.

Daraktan Sashen Kula da Sauran Cibiyoyin Kuɗi na CBN, Yemi Solaja, ya tabbatar da wannan ci gaba a birnin Legas yayin taron shekara-shekara na Kwamitin Shugabannin Ayyukan Bankuna.

Ya ce: “Cibiyoyi kamar Moniepoint MFB, Opay, Kuda Bank da sauran su yanzu an ɗaga musu matsayi. A zahiri, tun da farko suna gudanar da ayyukan su ne a duk faɗin ƙasar.”
Solaja ya kuma jaddada muhimmancin samun ofisoshi na zahiri domin tallafa wa abokan ciniki, inda ya bayyana cewa yawancin masu amfani da ayyukan waɗannan kamfanoni suna cikin ɓangaren tattalin arziƙin da ba na hukuma ba (informal sector).
Ya ce: “Yawancin abokan cinikin su suna aiki ne a ɓangaren da ba na hukuma ba. Don haka suna buƙatar wurin da za su iya kai ƙara ko samun taimako idan wata matsala ta taso.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *