Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci dukkan masu hadahadar mu’amalar kuɗaɗe da ‘Point of Sale’ (PoS) da kuma masu ba da sabis na biyan kuɗi da su tabbatar da haɗa na’urar PoS da lambar sirrin shaidar aikawa da kuɗi daga wani banki zuwa wani, wato ‘Nigeria Inter-Bank Settlement System’ (NIBSS) da kuma lambar bai-ɗaya mai tabbatar da shigar kuɗi asusun da aka tura shi cikin gaggawa, wato ‘Unified Payment Services Limited’ (UPSL) nan da kwanaki 30.
CBN ya ce an fito da wannan sabon umarni na baya-bayan nan ne domin magance yawaitar samun matsalolin tangarɗar kasawa ko ƙin shigar kuɗaɗe cikin asusun da aka tura su nan take, da ma sauran cikas ɗin da ake fuskanta yayin mu’amaloli a tsarin biyan kuɗi a ƙasar nan.
Wannan umarni na cikin wata sanarwa mai taken PSS/DIR/PUB/CIR/001/002, wadda Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi, Rakiya Yusuf, ta sanya wa hannu. Umarnin ya shafi dukkan masu karɓar biyan kuɗi masu sarrafa hadahadar kuɗi, masu tara sabis na na’urorin biyan kuɗi, da sauran masu ba da sabis da ke aiki a Nijeriya.
A cewar babban bankin, wannan tsari ya ginu ne bisa shawarar da CBN ya yanke a watan Satumba, 2024 na dakatar da dogaro da hanyar dogaro da tsarin mu’amala guda ɗaya, wanda bankin ya ce yana da babban tasiri wajen haddasa yawan katsewar sabis a tsarin biyan kuɗi na zamani a Nijeriya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a ƙarƙashin sabon tsari, dukkan masu PoS dole ne su riƙa haɗin kai da duka kamfanonin da aka ba lasisin tara sabis na na’urorin biyan kuɗi, wato NIBSS da UPSL, tare da daidaita tsarin su yadda zai iya sauya hanyar kasa wucewar kuɗin da aka tura kai-tsaye, wato ‘automatic failover’, idan wata hanya ta samu matsala. Wannan zai tabbatar da cewa ana ci gaba da mu’amala ba tare da tsaiko ba idan ɗaya daga cikin hanyoyin ta fadi.
CBN ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin rage yawan gazawar turawa da shigar kuɗaɗe daga wannan banki zuwa wani banki ta hanyar amfani da PoS da ke cutar da ‘yan kasuwa, masu saye da sayarwa, har ma da kamfanoni, musamman a sashen kasuwanci na dillalai da na kasuwar gargajiya, inda na’urorin PoS suke zama babbar hanyar biyan kuɗi.
Domin ƙarfafa juriyar tsarin da kuma tabbatar da bin doka, an umurci NIBSS da UPSL da su riƙa gudanar da gwaje-gwajen tsarin akai-akai tare da cibiyoyin kuɗi, sannan su miƙa rahoton sakamakon gwaje-gwajen ga CBN. Haka kuma, kamfanonin mu’amalar kuɗi biyu guda biyu dole ne su riƙa ba bankuna sanarwa kai-tsaye idan tsarin ya samu tangarda, tare da gabatar da cikakken rahoton abin da ya faru ga Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi cikin sa’o’i 24, ciki har da musabbabin matsalar da matakan gyara da aka ɗauka.
Wa’adin bin wannan umarni na kwanaki 30, wanda zai ƙare a tsakiyar watan Janairun 2026, ya sanya babban nauyi a kan masana’antar da ke sarrafa miliyoyin hadahadar kuɗaɗe a kowace rana. Yayin da Nijeriya ke hanzarta sauyawa zuwa tsarin hadahadar kuɗi ta zamani, wato dijital.
Gazawar mu’amalolin PoS ta ci gaba da zama babbar matsala duk da matakan da CBN ta taɓa ɗauka a baya, ciki har da ƙaddamar da buƙatar ‘geo-tagging’ a watan Agusta. Duk da cewa yawancin masu ruwa da tsaki a masana’antar sun yaba da umarnin haɗin kai a matsayin muhimmin mataki na daidaita ginshiƙin tsarin biyan kuɗi.
