Ashafa Murnai Barkiya
Tsare-tsaren Hada-hadar Kuɗaɗe a ƙarƙashin aiwatarwar Babban Bankin Nijeriya (CBN) na ci gaba da samun nasarorin haihuwar ‘ya’ya masu idanu, har ma da ‘yan tagwaye, yayin da farashin kayayyaki ya ƙara sauka ƙasa zuwa kashi 16.05 bisa 100 a watan Oktoba, daga kashi 18.2 bisa 100 a watan Satumba, 2025.
Shi kan sa malejin tsadar rayuwa ɗungurugum ya yi ƙasa sosai daga yadda yake a kashi 19.53 bisa 100 cikin Satumba, inda a watan Oktoba ya sauka zuwa kashi 18.69.
Malejin hauhawa da saukar farashi kuwa ya ƙara yin ƙasa sosai, daga kashi 13.57 bisa 100 a watan Satumba, inda a watan Oktoba malejin ya sauka ƙasa zuwa kashi 13.12 bisa 100.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje ya haura Dala biliyan 46.7, adadin da ba a taɓa samu ba tsawon shekaru 12 a baya.
Wannan nasara, sauƙi da rangwame tare da saitin tsarin hada-hadar kuɗaɗe a ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki, sun samu ne musabbabin kyawawan tsare-tsaren da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya bijiro da su.
Rabon da Asusun Kuɗaɗen Waje na Najeriya ya kai wannan adadin tun a ranar 13 ga Satumba, 2013, inda ya kai Dala 46.1.
A kasuwannin yankunan karkara farashin kayan abinci na ci gaba da sauka, musamman irin su wake, gero, masara, dawa da sauran su.
