Ashafa Murnai Barkiya
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bai wa masu lasisin hadahadar canjin kuɗi (BDC) damar samun kuɗaɗen ƙasashen waje daga Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje ta Nijeriya (NFEM) ta hannun bankunan da aka ba izini.
CBN ta sanar da hakan ne a ranar Talata cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Musa Narkoji, Daraktan Sashen Kasuwanci da Canjin Kuɗi, wadda aka aike wa dukkan bankunan da aka ba izini da kuma jama’a baki ɗaya.
Babban bankin ya ce dukkan BDC masu lasisi daga CBN za su iya sayen kuɗin ƙasashen waje daga NFEM ta kowanne banki da aka ba izini da suka zaɓa, a kan farashin kasuwa na lokacin.
A cewar takardar, an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara wadatar kuɗin waje a ɓangaren kasuwar sayar musayar kuɗaɗen waje, tare da biyan buƙatun kwastomomin da ba su kauce wa sharuɗɗa da ƙa’idoji ba.
“Bankunan da aka ba izini dole ne su kammala dukkan matakan sanin abokin hulɗa (KYC) da kuma bincike bisa ƙa’ida ga BDC ɗin da suke mu’amala da su, bisa dokoki da tsarin kula da haɗari na cikin gida,” cewar CBN.
“Bayan kammala waɗannan matakai, za a iya sayar wa BDC kuɗin waje domin amfani da shi bisa ga ƙa’idojin BDC na yanzu, amma kada ya wuce dala 150,000 a kowane mako ga kowanne BDC.
“Dukkan BDC masu lasisi su tabbatar da aikewa da rahotanni ga CBN ta hanyar isar da sako ta hanyoyin sadarwa na zamani, cikin lokaci da kuma daidai da dokokin da ake aiki da su.
“Duk wani kuɗin waje da ba a yi amfani da shi ba dole ne a mayar da shi kasuwa cikin awa 24 (ba a yarda BDC su riƙe kuɗin da suka saya daga NFEM ba).”
CBN ta ƙara da cewa duk mu’amalar canjin kuɗi tsakanin BDC, bankunan da aka ba izini, da kwastomomi, to fa dole ne a biya su ta asusun bankuna masu lasisi.
Haka kuma, CBN ya haramta mu’amala ta cinikin wuri-na-gugar-wuri, tare da cewa biyan kuɗi a tsabar kuɗi bai kamata ya wuce kashi 25 cikin 100 na kowace mu’amala ba.
CBN ya jaddada cewa duk mu’amalolin da ke ƙarƙashin wannan tsari za su kasance bisa ƙa’idojin aiki na BDC da ke nan a yanzu.
A ranar 20 ga Disamba 2024, CBN ya bai wa BDC damar wucin-gadi ta sayen dala 25,000 duk mako daga 19 ga Disamba 2024 zuwa 30 ga Janairu 2025.
A watan Fabrairu 2025, bankin ya tsawaita wa’adin damar da aka bai wa BDC masu cancanta don samun kuɗin waje daga hukuma.
