CBN ya yi alƙawarin samar da takardun Naira masu tsafta

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi alƙawarin ci gaba da aikin samar da takardun Naira masu tsafta.

Sannan kuma bankin ya ƙara yin kira ga ‘yan Nijeriya su riƙa ɗaukar Naira da daraja, su daina shafa wa takardun kuɗaɗe datti.

Wannan kira da alƙawari ya fito daga bakin Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Hakama Ali, a lokacin da take jawabi a Dandalin Bajekolin Ƙasa da Ƙasa na 20 a ranar Alhamis, a Abuja, Babban Birnin Tarayya.

Hakama wadda ta yi jawabin a Ranar CBN a wurin taron, ta ce “a riƙa yin hada-hada da naira cikin riƙon darattawa, a daina shafa mata datti. A daina yin liƙi, a daina sayar, a daina duƙunƙune ta, kuma a guji buga jabun kuɗaɗe.

“Sannan muna ƙara yin kira ku zama kyawawan jakadun Bankin CBN masu riƙe Naira da daraja. CBN ba zai iya wannan aiki shi kaɗai ba, sai da gudummawar ku. Naira ita ce abin alfaharin mu.

“Muna fatan ganin ci gaba da bada haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin hada-hadar kuɗaɗe. Samun wannan nasara abu ne da sai an haɗa hannu za mu iya shawo kan ƙalubalen saisaita tattalin arziki, domin mu samu ƙasaitacciyar bunƙasa,” inji ta.

Ta ce shugabannin CBN na ta bakin ƙoƙarin shawo kan matsalolin da za a kawar domin bunƙasa yawan kayan da ake sarrafawa a cikin gida da kuma ƙarfafa tattalin arziki.

Ta ce kaiwa ga ƙololuwar arzikin dogaro da kai ga ƙasa abu ne mai buƙatar shika-shikai uku da suka haɗa da, “tsarin harkokin kuɗaɗe mai ƙarfi, ingantacciyar kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗen waje da kuma haɗin guiwa mai ƙarfi tsakanin ɓangarorin kula da harkokin kuɗaɗe.

“Tuni an fara ganin kyakkyawan sakamako daga ƙoƙarin da CBN ke yi, ta inda har asusun kuɗaɗen waje ya kai Dala biliyan 43.05 tun a ranar 11 ga Satumba, 2025. Wato ya ƙaru daga Dala biliyan 40 ɗin da yake a ƙarshen watan Yuli, 2025.”

Ta ce CBN na ta ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki, yayin da zuwa yanzu manyan bankuna 14 sun cika sharuɗɗan mallakar Naira biliyan 500 a matsayin mafi ƙarancin jari. Ta ce CBN na ci gaba da tabbatar da sauran bankunan sun kammala cika sharuɗɗan cikin nasara.

An fara wannan bajekoli tun a ranar 25 ga Satumba, za a rufe a ranar 6 ga Oktoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *