Ashafa Murnai
Naira ta ci kasuwar ƙarshen watan Oktoba tare da samun galabar Naira 15.33 kan Dalar Amurka, a ranar 31 ga Oktoba.
Naira ta samu wannan tagomashin na Naira 15.33 a ranar Juma’a kan Dala a kasuwar ‘yan canji da kuma Hada-hadar Musayar Kuɗaɗe ta bai-ɗaya (NAFEM).
A Abuja dai an sayar da Dala $1 kan Naira 1450, yayin da masu canji suka saya kan Naira 1440.
An samu rangwame idan aka kwatanta da yadda aka sayi Dalar Amurka kan Naira 1,465 a ranar Alhamis.
Masu lura da kuma sharhi kan tattalin arzikin ƙasa da hada-hadar kuɗaɗe sun danganta wannan gwauron numfashi da Naira ta yi da irin ƙoƙarin da CBN yake kan yi wajen saisaitawa da daidaita farashin musayar kuɗaɗe.
