Cika Shekaru 25: Ministan Yaɗa Labarai ya jinjina wa tasirin ƙungiyar ActionAid cikin al’umma
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa ƙungiyar nan mai zaman kan ta ta ActionAid Nigeria bisa cika shekaru 25 da ta yi tana aiki, hidima, da ayyukan sauyi a faɗin ƙasar nan.
Da yake jawabi a bikin cika shekaru 25 da kafuwar ƙungiyar a Abuja a ranar Alhamis, Ministan ya ce, “An samu tsawon rabin ƙarni, ActionAid ta kai ci gaba zuwa matakin farko, tana ba mata da ‘yan mata ƙarfi, tana ƙarfafa ilimi, inganta kiwon lafiya, yin rajin gyaran shugabanci, tallafa wa al’umma a lokutan rikice-rikice, da kuma ƙara wa muryar masu rauni ƙarfi.”
Ya ƙara da cewa ya kamata a yaba wa ActionAid bisa yawan martanin da ta ba mawuyacin halin jinƙai da kuma ayyukan ƙara wa al’umma ƙarfi daga tushe—waɗanda suka sauya manufofi da cigaban al’umma ta hanyoyi masu zurfi da auna tasirin su a Nijeriya.
Ya ce: “A yau, mun taru ne don girmama wannan gado tare da duban babi na gaba.”
Ya jaddada muhimmancin manyan abubuwa guda biyu da aka gabatar a bikin: ƙaddamar da littafin “AAN@25 Legacy Book” da kuma bayyana sabon tsari na ginin ActionAid, yana bayyana su a matsayin alamar bunƙasar ƙungiyar da yaruwar ta a tsawon lokaci a Nijeriya.
Idris ya ce: “Ina kuma farin cikin bayyana tsarin ginin ActionAid, wata alama mai ƙarfi ta bunƙasar ƙungiyar da ɗorewar ta na dogon lokaci a Nijeriya. Wannan jarin da ke kallon gaba yana nuna jajircewar ActionAid wajen zurfafa gudunmawar da take bayarwa ga ƙasar mu a shekaru 25 masu zuwa da ma bayan haka. Waɗannan nasarori sun cancanci caffa da yawan yabo.”
Yayin da yake warware wani kuskuren fahimta game da Nijeriya a ƙasashen waje, Idris ya jaddada cewa ƙasar nan ba mai tauye ‘yancin addini ba ce, kuma ya tabbatar da cewa irin wannan ‘yanci ya samu cikakken tanadi a kundin tsarin mulki.
Ya jaddada cewa akwai ƙalubalen tsaro, amma ya ce ƙoƙarin gwamnati na kawo ɗa’a yana haifar da sakamako.
Ya gargaɗi masu yaɗa labarai marasa inganci da ke nuna Nijeriya ta wani mummunan salo, wanda hakan kan jawo matsala a hulɗar ta da abokan ta, musamman Amurka.
Ya roƙi ƙungiyoyi masu zaman kan su da su taimaka wajen gyara irin wannan mummunar fassarar ta hanyar amfani da hujjoji na gaskiya waɗanda za su ba su damar taka muhimmiyar rawa ta gini da jagoranci wajen sake fasalin labaran bogi da ake yaɗawa.
Yayin da ya tabbatar da nauyin da gwamnati take da shi na kare ‘yan ƙasa, musamman yara, ya jaddada cewa “ya kamata a kiyaye yaran mu a makarantun su, a cikin al’ummomin su, da kuma a gidajen su,” tare da jaddada sanarwar da Shugaba Tinubu ya yi kwanan nan kan dokar ta-ɓaci a fannin tsaro.
Ministan ya bayyana cewa matakan dokar ta-ɓaci sun haɗa da ɗaukar sababbin jami’ai a hukumomin tsaro, tallafa wa rundunonin tsaro na jihohi, da kuma tura ƙudirin doka domin kafa ‘yan sandan jihohi.
Ya bayyana wannan sanarwa a matsayin muhimmin mataki na juyin-juya-hali a yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga.
Ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kan su (CSOs) da su zurfafa goyon bayan su ga shugabanci na fayyace komai, ‘yancin kafafen yaɗa labarai, ilimin zamani na dijital, da cigaban al’umma, tare da tabbatar da cewa gudunmawar ActionAid a waɗannan fannoni “na cike da muhimmanci kuma ba za a iya musanta ta ba” wajen cigaban ƙasa.
