Cire Tallafin Mai Ya Taimaka Mana Wajen Aiwatar da Ayyuka, Inji Gwamna

Gwamnan Jihar Inugu, Mista Peter Mbah, ya ce gwamnatin jihar sa ta samu damar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a fadar Gwamnatin Jihar Inugu, lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar sa a ziyarar ban-girma da suka kai masa.

Tawagar ta je jihar ne domin shirin taron tattaunawa tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan ƙasa na tsawon kwanaki biyu a yankin Kudu-maso-gabas.

Ya ce: “A Inugu, mun sami damar cika duk abin da muka yi wa mutanen mu alƙawari a lokacin kamfen, godiya ga jarumtar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wadda ta samar mana da albarkatun da ake buƙata don aiwatar da manyan ayyuka.”

Ya kuma bayyana ayyukan da ake yi a halin yanzu a jihar, waɗanda suka haɗa da gina ajujuwa 7,000, samar gadajen asibiti 3,300, da samar da gonakin gwamnati hekta 2,000 a cikin gundumomi 260 na jihar.

Gwamna Mbah ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa manufofin Gwamnatin Tarayya baya, yana mai cewa suna da amfani ga al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *