CNPP a Kaduna ta yi tir da kiran AYCF na neman a ayyana dokar ta-baci a Zamfara

Ƙungiyar CNPP reshen Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Mallam Mikailu Abubakar ta yi kakkausar suka tare da yin Alla-wadai da kiran da Ƙungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi na a ƙaƙaba dokar ta-baci a Jihar Zamfara.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Ambasada Sanin Yaya ya fitar.

Sanarwar ta ce; “Rashin tsaro na haifa da ƙalubale a faɗin jihohi daban-daban, don haka ƙungiyar CNPP ta yi imanin cewa kiran a kafa dokar ta-baci wani mataki ne da zai iya ƙara dagula tsarin mulki da kuma kawo cikas ga dimokuraɗiyya a Zamfara.

“Al’ummar jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal sun ci gaba da nuna jajircewa wajen fuskantar barazanar tsaro. Maimakon yin zagon ƙasa ga gwamnatin farar hula ta hanyar kiraye-kirayen da ba dole ba na neman a ayyana dokar ta-baci, ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai don ƙarfafa ayyukan cikin gida da nufin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Ƙungiyar CNPP ta tabbatar da cewa al’amuran tsaro na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi ba wai ruguza tsarin dimokuraɗiyya da ake kai ba. Muna yin taka tsantsan game da siyasantar da rashin tsaro, muna kuma kira ga dukkan ƙungiyoyin da abin ya shafa, ciki har da AYCF, da su yi aiki da hankali don gujewa ɗaukar tsauraran matakan da ka iya cutar da jihar da al’ummarta.

“Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da irin waɗannan kiraye-kirayen, maimakon haka ya ƙara ba gwamnatin jihar Zamfara tallafin kayan aiki da fasaha a yaƙin da take yi da rashin tsaro.

“Ƙungiyar CNPP a jihar Kaduna ta ci gaba da jajircewa wajen inganta dimokuraɗiyya, zaman lafiya, da shugabanci nagari a faɗin Nijeriya,” inji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *