Darajar Naira na cigaba da farfadowa inda farashin Dollar ya karye zuwa Naira 1,534

An samu sabbin labarai masu dadi dangane da darajar Naira a kasuwar musayar kudade, inda ta ƙara daraja a karshen mako, yanayin da ke nuna alamar ci gaba da farfadowar tattalin arzikin kasa.

A ranar Juma’a, Naira ta rufe kasuwa a Naira 1,534.72 a kan kowace Dala guda, bisa rahoton sabbin alkaluman da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar. Wannan ya nuna karuwar Naira 4 da Kobo 52, wanda ke nuni da ci gaba, duk da karancin bambanci da ranar Alhamis.

Masana tattalin arziki da ‘yan kasuwa sun bayyana jin dadinsu, tare fatan wannan ci gaba zai dore tare da habaka amincewa da Naira a kasuwar duniya. A cewarsu, wannan karin daraja yana karfafa zuciyar ‘yan kasuwa da masu zuba jari, yana kuma bayyana nasarar matakan sauye-sauye da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *