Gobara ba ta tashi a Hedikwatar CBN ba

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) na sanar da cewa labarin da wasu marasa kishin ƙasa suka yaɗa a soshiyal midiya cewa hedikwatar bankin ta kama da wuta, ƙarya ce, babu abin da ya faru a bankin.

Wata taƙaitacciyar sanarwar da CBN ya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Lahadi, ta ce labarin na bogi ne, kuma hoton da aka buga a soshiyal midiya mai nuni da kamar wuta ta tashi a saman ginin hedikwatar bankin, duk ƙarya ce, na bogi ne, kuma ƙirƙira ce wasu suka yi.

Saboda haka CBN ya roƙi jama’a cewa kowa ya kwantar da hankalin sa, babu wani abu da ya samu bankin. Sanarwar ta kuma roƙi a yi watsi da irin waɗannan labarai da hotuna na bogi a duk inda aka ci karo da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *