Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Dare Lawal, ya bayyana alhini mai zurfi bayan samun rahoton kisan jami’an tsaro takwas da ’yan bindiga suka yi a hanyar Funtuwa zuwa Gusau.

Rahoton ya bayyana cewa harin ya shafi jami’an ‘yan sanda da Askarawan Zamfara.

A shafin sa na Facebook, Gwamna Lawal ya rubuta: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Na samu rahoto mara daɗi na kwanton ɓauna da ’yan bindiga suka yi wa jami’an tsaron ’yan sanda da Askarawan Zamfara a hanyar Funtuwa zuwa Gusau, inda suka kashe jami’ai takwas. Allah (T) Ya jiƙan su, Ya ba iyalai da ’yan uwan su haƙurin wannan rashi.

Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya gaba ɗaya.”

Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *