Gwamnan CBN ya bayyana alfanun bai wa Nijeriya kujerar dindindin a Hukumar Gudanarwar Cibiyar Kuɗi ta Afrika

Ashafa Murnai Barkiya

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya yaba da amincewar da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi na ba Nijeriya kujerar dindindin a Hukumar Gudanarwar Cibiyar Kuɗi ta Afirka (AMI).

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana matuƙar farin cikin sa kan matakin da taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) karo na 39 ya ɗauka na amincewa da zama mamba ta dindindin na Njeriya a Hukumar Gudanarwar Cibiyar Kuɗi ta Afirka (AMI).

An yanke wannan shawarar ce a taron ƙoli na watan Fabrairu 2026 da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Amincewar ta biyo bayan sahalewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Afirka ta yi a zaman ta na 48.

Cardoso ya bayyana wannan ci gaba a matsayin nasara ga Nijeriya da kuma babban mataki ga haɗin kan Afirka da ‘yancin kuɗaɗen nahiyar.

Cibiyar AMI, wadda aka kafa a ƙarƙashin shirin cibiyoyin kuɗi na AU, ana kallon ta a matsayin mataki na share fage ga kafuwar Babban Bankin Afirka (ACB), wanda za a kafa hedikwatar sa a Abuja, Nijeriya.

Gwamnan CBN ya jaddada cewa karɓar baƙuncin AMI da kuma ACB nan gaba na da matuƙar muhimmanci ga Nijeriya da ma nahiyar baki ɗaya.

Ya ce hakan zai ƙara wa Nijeriya tasiri da murya wajen tsara tsarin kuɗi guda na bai-daya na Afirka.

Haka kuma Cardoso ya yaba wa matakin da ya ba Nijeriya damar zama mamba ta dindindin a Majalisar Daidaiton Tattalin Arziki, inda Cardoso ɗin ya ce wannan hukunci na tarihi wata muhimmiyar alama ce a tafiyar Afirka ta haɗin kan harkokin kuɗi tare bai-daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *