Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karyata kalaman Shugaban Amurka, Donald J. Trump, da ya yi ikirarin cewa ana kashe Kiristoci da yawa a Najeriya, tare da kira da a sanya kasar cikin jerin kasashen da ke take hakkin addini.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, mai dauke da sa hannun Kimiebi Imomotimi Ebienfa, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, gwamnatin ta ce kalaman Trump ba sa nuni ga ainihin halin da ake ciki a kasar ba.
Sanarwar ta ce: “Najeriya tana godiya da damuwar kasashen duniya game da kare hakkin bil’adama da ‘yancin addini, amma wannan ikirari ba shi da tushe. ‘Yan Najeriya mabiya dukkan addinai suna rayuwa, aiki da kuma ibada tare cikin lumana.”
Ma’aikatar ta kara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen yaki da ta’addanci, karfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da hakkokin dukkan ‘yan kasa.
Najeriya ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka domin inganta fahimtar juna kan harkokin yankin da kuma kokarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
