Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shatima ne ya bayyana buƙatar a yayinda ya yi wata ganawa da tawagar bankin a fadar Shugaban Kasa,
Mataimakin shugaban yayi nuni da yadda Najeriya ta sami bunkasa a harkokin kasuwanci a karkashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da irin kokarin da gwamnati ke yi na magance kalubalen da ake fuskanta a muhimman ɓangarorin tattalin arziki da suka hadar da zuba jari akan ƴan kasa da samar da abinci mai gina jiki, da bunkasa noma, da kiwon lafiya, da ilimi, da kasuwanci na zamani inda ya karfafa wa bankin gwiwar kan yin amfani da yanayin da ake ciki a matsayin lokaci mafi dacewa na zuba jari a Najeriya, yana mai nuni da sauye-sauye a sassa masu mahimmanci da gwamnatin ta samar
Baya da bunkasa tattalin arzikin Halal, Kashim Shettima ya bukaci bankin da ya inganta kasuwanci a bangaren fasahar zamani, da hada-hadar kudi da sabon shirin Agro-Processing Zones (SAPZ) na samar da muhalli na musamman ga noma da ilmi da ababen more rayuwa da kiwon lafiya.
Ita ma Tawagar bankin Musulunci, karkashin jagorancin Mista Hammad Hundal, ta nuna gamsuwarta da tsare-tsaren gwamnatin shugaba Tinubu inda ta bayyana kudurinta na fifita ƙudurorin Shugaban a matsayin hanyar haɓaka farfado da walwala da magance talauci, da kuma haifar da ci gaban tattalin arziƙin.