Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Samu Goyon Bayan China Don Gina Masana’antun Motocin Lantarki a Najeriya

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu babbar nasara a kokarinta na fadada tattalin arzikin kasa, yayin da kasar China ta bayyana aniyarta na kafa masana’antun kera motocin lantarki (EV) a Najeriya. Wannan sanarwa ta fito ne lokacin da Jakadan China a Najeriya, Mista Yu Dunhai, ya kai ziyarar girmamawa ga Ministan Bunƙasa Ma’adanai, Dr. Dele Alake.

Wannan mataki ya biyo bayan ganawar manyan shugabanni tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Xi Jinping na China, inda suka yanke shawarar inganta dangantakar kasashen biyu zuwa matakin cikakken hadin gwiwar dabarun ci gaba. Jakada Dunhai ya yabawa albarkatun kasa masu yawa da Najeriya ke da su, tare da bayyana shirye shiryen kasar China na kara zurfafa hadin gwiwa a bangaren ma’adanai, musamman daidai da burin Shugaba Tinubu na kara darajar albarkatu a cikin gida da bunkasa masana’antu.

Jakadan ya bayyana cewa kamfanonin kasar China tuni suna aiki a fannin haka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *