Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da kamfen ɗin “Nijeriya ta, Ɗabi’a ta”

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon kamfen na ƙasa baki ɗaya domin ƙarfafa wa ’yan Nijeriya gwiwa su nuna kishin ƙasa ta hanyar nuna kyakkyawar ɗabi’a, riƙon gaskiya, da yin ayyukan da ke taimaka awa cigaban ƙasa a kullum.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya ƙaddamar da shirin mai taken “Nijeriya ta, Ɗabi’a ta” a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Kamfen ɗin, wanda Ofishin Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin ’Yan Ƙasa da Jagoranci ya jagoranta, manufar sa ita ce farfaɗo da ɗabi’ar kyakkyawar ɗabi’a ga ƙasa, tare da jaddada cewa kowa yana da rawar da zai iya takawa kai-tsaye wajen gina martabar Nijeriya, cigaban ta, da tafiyar dimokiraɗiyya.

Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙasa, Ministan ya bayyana kishin ƙasa a matsayin “fi’ili mai aiki”, yana mai cewa ana nuna shi ne ta hanyar ɗabi’a, biyan haraji, guje wa yaɗa labaran ƙarya, da jajircewa wajen cigaban ƙasa.

“Kishin Ƙasa na gaske shi ne zaɓin da mutum ke yi a kullum na bayyana kyakkyawar ɗabi’a, labarin ƙasar mu, cigaban ta, da martabar ta,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “Makomar Nijeriya ba a hannun mutane kaɗan take ba, tana cikin ayyukan jama’ar ƙasa miliyan 200 ne.”

Idris ya kuma jaddada goyon bayan da Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayar wajen kare dimokiraɗiyya tsawon shekaru, yana mai cewa rayuwar sa ta siyasa tana nuna ruhin kyakkyawar ɗabi’a da kamfen ɗin yake son a yaɗa a faɗin ƙasar nan.

Ya danganta manyan gyare-gyaren da gwamnati ta yi kamar cire tallafin mai, gyaran tsarin canjin kuɗi, tsarin adalcin haraji, da tattara kuɗaɗen shiga ta hanyar dijital da manufar samar da cigaba da ya shafi kowa.

Ya ce, “Da gaske akwai wahala, amma wahalar farfaɗowa ce, ba ta lalacewa ba.”

Ya yi bayanin cewa kuɗaɗen shiga da ake raba wa gwamnatoci (FAAC) sun ninka fiye da sau biyu, abin da ya bai wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin dama wajen inganta kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da ababen more rayuwa.

Yayin da ya yi magana kan biyan haraji, ya ce abin yana da alaƙa kai-tsaye da cigaban ƙasa, ya ce: “Kishin ƙasa na cikin harajin da kuke biya ne. Idan kuka biya harajin ku, kuna zuba jari ne kai-tsaye a makarantar da ɗan ku ke zuwa ne, hanyar da kasuwancin ku ke amfani da ita, da tsaron da ke kare gidan ku.”

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa a Fabrairun 2026 za a ƙaddamar da Cibiyar Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai (MIL) ta Ƙasa, domin inganta sadarwa mai kyau da yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya.

Ya ce: “Kada mu yi amfani da ƙarya a matsayin makami. A wannan zamani na dijital, sadarwa ta gaskiya aikin kishin ƙasa ne.”

Idris ya yi kira ga ’yan ƙasa da su rungumi ƙa’idojin da ke cikin Sabuwar Yarjejeniyar Zama Ɗan Kasa, wadda ta ƙunshi tsare gaskiya, kishin ƙasa, himma, haƙuri, da kyakkyawan aiki, tare da ɗaukar kamfen ɗin a matsayin alƙawari na haɗin kan gina ƙasa.

A ƙarshe ya ce: “Shugaban Ƙasa yana shimfiɗa tubalin daidaito da hangen nesa. Mu haɗa hannu mu zana sabuwar Nijeriya mai kyau ta hanyar ɗabi’un mu, harajin mu, labaran mu, da ayyukan mu. Nijeriya ta, Ɗabi’a ta.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *