Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Shirin Ba da Lamuni Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu da Kiwon Lafiya Kyauta Ga Masu Ritaya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ƙaddamar da shirye-shirye biyu na jinƙai ga ma’aikatan ilimi da masu ritaya, wanda ya haɗa da bayar da lamuni ga ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma polytechnic, da kuma samar da kiwon lafiya kyauta ga masu karamin albashi da suka yi ritaya.

Shirin farko, mai suna Asusun Tallafin Ma’aikatan Manyan Makarantun Gaba Da Sakandire wato ‘Tertiary Institution Staff Support Fund’ (TISSF), zai bai wa malamai da ma’aikata da basa koyarwa damar samun lamuni domin biyan bukatun yau da kullum a farashi dake ƙasa da na bankunan kasuwanci.

Shirin na biyu zai bai wa masu ritaya masu ƙaramin ƙarfi damar samun kiwon lafiya kyauta karkashin Tsarin Fansho na Gudummawar Hadin Gwiwa wato Contributory Pension Scheme. Gwamnati ta bayyana cewa wannan shiri zai kawar da kashe kuɗi daga aljihun masu ritaya wajen samun magani a asibitocin da aka ware, ta yadda za su samu kulawar lafiya ba tare da wani kuɗi ba.

Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar cewa za a rika samun kuɗin gudanar da shirye-shiryen ta hanyar kasafin kuɗi da wasu kudade na musamman, tare da kulawar ma’aikatun gwamnati da abin ya shafa don tabbatar da gaskiya da inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *