Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikatan Koyar da Sana’o’i a Kwalejojin Fasaha

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar Masu Koyar da Sana’o’in Fasaha (Technical Facilitators) a Kwalejojin Fasaha na Gwamnatin Tarayya da ke fadin ƙasar nan, a wani mataki na musamman na tsawon shekara guda domin farfaɗo da tsarin koyar da sana’o’i.

Ma’aikatar ta ce wannan shiri na daga cikin manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin cike gibin ƙwarewar sana’o’i a Najeriya ta hanyar jawo ƙwararrun masana daga fannoni daban-daban na sana’a da masana’antu domin koyar da ilimin zamani bisa ka’idojin kwarewa (competency-based training).

Sanarwar ta bayyana cewa ana neman ƙwararrun masana fasaha masu kwarewa tare da iya koyarwa, domin inganta koyar da darussa na aikace-aikace da na ka’ida a Kwalejojin Fasaha na Tarayya. Wannan shiri na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin tabbatar da cewa ilimin fasaha ya dace da bukatun kasuwar aiki ta zamani.

Ma’aikatar ta bukaci duk masu sha’awar neman aikin da su cike takardar neman aiki ta yanar gizo ta shafin dake ƙasa.

https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSfxRAdsj9oBzdkmbKsYiei30L5o8aH-QhHo1UFMCVlL0i6BEw/viewform?pli=1&fbclid=IwdGRjcAQCYbRleHRuA2FlbQExAHNydGMGYXBwX2lkCjY2Mjg1NjgzNzkAAR69uyV9ksgzQnC8wo5MECkwUBS-eIq_0zBFPYt5MyBFIi8eaKv2qCpqr9WRFw_aem_yaCzbQ3dgl-RVgM4BsbpvA

Ta jaddada cewa za a tantance dukkan rejistar da aka tura bisa cancanta da kwarewa.

An sanar da cewa za a rufe shafin neman aikin da karfe 11:59 na dare ranar Litinin, 16 ga Maris, 2026.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sake jaddada kudirinta na mayar da Kwalejojin Fasaha na Tarayya cibiyoyin ƙwarewa wajen haɓaka sana’o’i, kirkire-kirkire da shirya matasa domin samun aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *