Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da wutar lantarki daga hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Makamashi ta Ƙasa (ECN) Dr Mustapha Abdullahi ya ce wutar lantarkin mai ƙarfin Megawatt huɗu (4MW) za ta bai asibitin damar rabuwa da layin wutar lantarki na ƙasa baki ɗaya.

Dr Mustapha Abdullahi, ya ce aikin na daga cikin manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa wannan tsari zai kawo ƙarshen matsalar yawan yanke wuta a asibitin, lamarin da a baya ya haddasa asarar rayukan marasa lafiya guda uku a lokacin da ayyukan asibitin suka tsaya cak.

“Da wannan tsari, ba za a sake samun irin waɗannan matsaloli ba. Burinmu shi ne mu samar da makamashi mai tsafta da nagarta wanda zai ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya tare da inganta rayuwar ’yan Najeriya,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *