Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na inganta harkar ilimi a Najeriya ta hanyar aiwatar da sauye-sauye da kuma tallafi daga sassa daban-daban.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin Jami’ar Ibadan (UI) a fadar shugaban ƙasa, Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Kayode Adebowale.
A wajen ziyarar, an karrama Shettima da lambar yabo mafi girma ta jami’ar, (UI at 75 Ambassador Plenipotentiary) a matsayin girmamawa ga gudunmawarsa a fagen hidimar jama’a da ƙasa baki ɗaya.
Shettima, wanda ya karanci Digirin Digirgir na Farko a fannin Tattalin Arzikin Noma daga UI a shekarar 1991, ya bayyana jami’ar a matsayin “babbar cibiyar koyo mafi girma a Yammacin Afirka,” yana mai tunawa da tasirin jami’ar a duniya baki ɗaya.
Ya jaddada cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na da ƙudirin ganin an hada kai tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin ɗaukaka jami’o’i kamar ta Ibadan da sauran cibiyoyin ilimi a Najeriya.
A ƙarshe, Shettima ya bayyana wasu daga cikin muhimman matakan sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa, ciki har da Nigerian Education Loan Fund (NELFUND) da aka kirkiro domin tallafawa ɗaliban da ke cikin ƙalubalen rashin kuɗi. Ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu domin ceto harkar ilimi daga matsalolin da ta shiga.
Haka kuma, ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasa yana samun ci gaba, inda ya ce an riga an wuce gaɓar ƙalubale.