Gwamnatin Tarayya Ta Raba Sama da Naira Biliyan 80 Ga Dalibai 400,000 — NELFUND

Shugaban Hukumar Lamunin Dalibai ta Kasa (NELFUND), Akintunde Sawyerr, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta riga ta raba fiye da naira biliyan 80 ga cibiyoyin ilimi daban-daban a Najeriya domin tallafa wa dalibai da lamunin biyan kudin makaranta. Ya bayyana cewa kimanin dalinai 745,000 ne suka nemi lamunin, inda a yanzu fiye da dalibai 400,000 suka amfana da lamunin. Wasu daga cikin daliban suna samun biyan kudin makaranta kai tsaye zuwa jami’o’in su, sannan masu neman tallafin kashe kuɗi suna karɓar N20,000 a kowane wata cikin zangon karatu.

Sawyer ya bayyana cewa duk lamunin da ake bayarwa ba su da kudin ruwa a kansu. Ya ce akwai nau’i biyu na lamuni, na biyan kudin makaranta wanda ake turawa kai tsaye ga makaranta, da kuma na tallafin kudin kashewa ga ɗalibi.

A cewar Sawyer, shirin NELFUND na taimaka wa dalibai yana rage yawan masu daina zuwa makaranta a matakin gaba da sakandare saboda ƙarancin kuɗi. Ya ce hukumar tana ci gaba da karɓar sabbin masu rejista, inda cikin sa’o’i 24 da suka wuce kadai aka samu sama da 2,700 daga sabbin dalibai sun nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *