Gwamnatin Tarayya ta taya ’yan Nijeriya murnar Kirsimeti, ta yi kira a yi haɗin kai da tausayi

Gwamnatin Tarayya ta taya jama’ar ƙasar nan, musamman mabiya addinin Kirista, murnar bikin Kirsimeti, inda ta bayyana lokacin a matsayin na ƙauna, sadaukarwa da kyakkyawar fata, tare da kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da nuna haɗin kai da tausayi duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar a ranar Laraba.

A cewar Ministan, darussan da bikin Kirsimeti ke koyarwa suna tunatar da ’yan Nijeriya muhimmancin kula da juna, zama tsintsiya-maɗaurin-ki-ɗaya, da kuma ci gaba da yarda da makomar ƙasar nan, ko da a lokutan wahala.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana daraja juriya da jajircewar ’yan Nijeriya, tare da jaddada cewa ba za a raina haƙurin da suka yi ko wahalhalun da suka sha ba.

“Haƙuri da juriya da ’yan Nijeriya suka nuna ba za a ɗauke su da wasa ba, haka kuma zufa da gumin su ba zai tafi a banza ba,” inji sanarwar.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da maida hankali wajen gina Nijeriya mai tsaro, ƙarfi da wadata, wacce za ta amfani kowa da kowa.

Ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen tunawa da waɗanda suke fuskantar matsaloli a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da yin addu’a ga iyalan da hare-haren ta’addanci suka shafa.

Haka kuma, Idris ya buƙaci jama’a da su saka jami’an tsaro a addu’oin su, yana mai yaba wa jajircewar su wajen kare rayuka, dukiyoyi da ƙasar daga barazana iri-iri.

“Yayin da muke murnar wannan lokaci, mu tuna da waɗanda ke cikin ƙalubale, mu yi addu’a ga iyalan da hare-haren ta’addanci ya shafa, sannan mu riƙa tunawa da jami’an tsaron mu waɗanda ke ci gaba da kare rayukan mu, dukiyoyin mu da ƙasar mu daga kowace irin barazana,” inji shi.

Gwamnatin Tarayya ta kuma ƙarfafa ’yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara haɓaka zaman lafiya, tausayi, da haɗin kai a cikin gidajen su da al’ummomin su, tana mai cewa haɗin kan ƙasa muhimmin ginshiƙi ne na ci gaba da ɗorewar zaman lafiya.

Ya ce: “Mu yi amfani da wannan lokaci wajen inganta zaman lafiya, kyautatawa da haɗin kai a cikin gidajen mu da al’ummomin mu.”

Ya kammala da yi wa ’yan Nijeriya fatan murnar Kirsimeti cikin annashuwa da kuma sabuwar shekara mai albarka, tare da yin addu’ar Allah Ya albarkaci Nijeriya.

“Barka da Kirsimeti da kuma sabuwar shekara mai albarka. Allah Ya albarkace ku baki ɗaya. Allah Ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya,” inji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *