Gwamnatin tarayya ta yi alhinin rasuwar mutanen da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a Ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja

Gwamnatin tarayya ta yi alhinin rasuwar mutanen da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, wanda rahotanni suka ce mutane 30 ne suka mutu.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya jajantawa gwamnati ga iyalan wadanda abin ya shafa, gwamnati da al’ummar jihar Neja.

Ministan ya yaba wa gwamnatin jihar Neja, ta hannun hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, bisa gaggauwa da aikin ceton da ta yi, wanda ya tabbatar da an kididdige duk fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen.

Ya kuma bukaci fasinjoji da su ba da fifiko wajen kula a kodayaushe yayin tafiya kan ruwa na cikin gida.

A cewar ministan, gwamnatin tarayya ta umurci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA da ta gudanar da wani gagarumin gangamin wayar da kan jama’a a fadin kasar domin wayar da kan al’umma kan matakan kariya a lokacin da ake amfani da magudanar ruwa a cikin ruwa.

Jirgin ruwan katako wanda aka ruwaito yana dauke da fasinjoji 138 a ranar Talata, ya kife ne a hanyar Shagunu zuwa Dunga a tafkin Kainji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *