GWAMNATIN TARAYYA ZA TA KAMMALA GYARAN ALAU DAM AKAN KUDI NAIRA BILIYAN 80 NAN DA 2027, DON INGANTA NOMAN RANI DA SAMAR WUTAR LANTARKI

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin gyare-gyare da fadada Alau Dam da ke jihar Borno, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 80, zai kammala nan da shekarar 2027. Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar aiki da ya kai wurin aikin a garin Alau, kusa da Maiduguri. Ya ce an fara aikin ne da amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu karkashin shirin Renewed Hope Agenda, domin Dan din ya zama mai amfanarwa sosai, ciki har da ban ruwa don bunkasa noman rani da kuma shirin samar da wutar lantarki a nan gaba.

Ministan ya bayyana cewa aikin ya kasu kashi biyu, inda kashi na farko zai kare a watan Satumba na wannan shekara, domin rage hadarin ambaliyar ruwa a wannan damina. Kashi na biyu kuma zai fara a watan Oktoba kuma ya kammala a watan Maris 2027, wanda zai kai ga kammala sake ginawa da fadada Dam din. Ya ce, bayan kammala aikin, Dam din zai kara inganta samar da ruwan sha ga Maiduguri da kewaye, ya tallafa wa noman rani, tare da bai wa yankin damar samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa.

Farfesa Utsev ya gode wa Shugaba Tinubu da Gwamna Babagana Umara Zulum bisa jajircewa wajen ganin aikin ya tabbata, yana kuma kira ga manoma a yankin su daina shuka amfanin gona a gefen Dam din domin kauce wa matsaloli yayin aikin. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kan yiwuwar ambaliya, yana mai bayyana cewa aikin na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin ruwa da inganta harkokin noma a Borno da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *