.
Gwamnatin Tarayya ta kasafta jimillar naira biliyan 493 domin wasu muhimman ayyuka biyu: kammala hanyar Kano zuwa Katsina mai tsawon kilomita 152 da kuma gina sabuwar Gadar Carter a Jihar Legas.
Ministan Ayyuka, David Umahi, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba, 13 ga Agusta, 2025.
Ministan ya ce an yi babban ƙari a kuɗin aikin hanyar Kano zuwa Katsina saboda yanayin tattalin arziki da ake ciki.
Umahi ya ce a da, gwamnatin da ta gabata ta raba aikin hanyar ne gida biyu.
Ya ce: “Sashe na Ɗaya, mai tsawon kilomita 74.1, da farko an ba da kwangilar sa ne a cikin 2013 a kan kuɗi naira biliyan 14, aka ƙara shi zuwa naira biliyan 24. To yanzu kuma an ƙara shi zuwa naira biliyan 68.
“Sashe na Biyu, mai tsawon kilomita 79.5 da aka bayar a cikin 2019 a kan kuɗi naira biliyan 29, aka ƙara shi zuwa naira biliyan 46, yanzu kuma ya koma naira biliyan 66.115.”
Jimillar kuɗin ayyukan a yanzu shi ne kimanin naira biliyan 134, sannan aka kasafta naira biliyan 6 a Kasafin Kuɗin shekarar 2024 da naira biliyan 34 a Kasafin Kuɗin 2025 don Sashe na Ɗaya. Shi kuma Sashe na Biyu an ware masa naira biliyan 80 a tsawon waɗannan shekaru biyu.
A game da Gadar Carter kuwa, Umahi ya ce daga binciken ƙarƙashin ruwa da aka gudanar a shekarun 2013 da 2019, an gano cewa masu haƙar ma’adinai ba bisa doka ba da kuma zaizayar ƙasa sun yi wa jikin gadar da turakun ta lahani sosai.
Kamfanin Julius Berger, wanda shi ne ke da alhakin yi wa gadar gyara a ƙarƙashin ruwa da tuwasun ta, ya ba da shawarar cewa gadar ta wuce a ceto ta, abin da ya kamata kawai shi ne a sake gina ta baki ɗaya.
Ita dai Gadar Carter, an gina ta ne a cikin 1901, kuma tana daga cikin manyan gadoji uku da suka haɗa Tsibirin Legas (wato Island) da babban garin Legas. Sauran su ne Gadar Third Mainland da Gadar Eko.
An raɗa mata sunan Sir Gilbert Thomas Carter ne, wani gwamnan Legas na zamanin mulkin mallaka.
An sha yi mata gyare-gyare bayan samun mulkin kai, domin a shekarun 1970 ma sai da aka kwance ta gaba ɗaya sannan aka sake haɗa ta.