Gwamnatin Tinubu Za ta Gaggauta Ba da Lamunin Naira Bilyan 250 Ga Manoma

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin lamunin Naira biliyan 250 ga kananan manoma a fadin Najeriya.

Umarnin, wanda aka bai wa Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Fadar Shugaban Kasa (PFSCU), na zuwa ne da nufin hanzarta rabon bashin wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, don bunkasa noman rani a yayin da ake tsaka da damuna don tabbatar da ci gaba da samar da wadataccen abinci ba tare da kakkautawa ba

Mataimakin Shugaban kasar ya gargaɗi hukumar da cewa dole ta gaggauta samar da tsarin aiwatar da rabon lamunin ta inda kudaden za su kai ga manoman da abin ya shafa ba tare da jan ƙafa ba, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci gafara-sa ba ta ga ƙaho ba.
A cewarsa ” Gwamnatin Shugaba Tinubu ta samar da shirin ne don ganin ƴan Najeriya sun amfana akan lokaci ba don ajiyar kudade ba”

Shettima, wanda ya yaba wa irin gudunmawar da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar PFSCU don yin gyaran-fuska ga tsare-tsaren samar da abinci ba tare da tarnaki ba musamman a bangaren sassauta hanyoyin samar da kayan haɗa taki da kafa asusun tallafin Shugaban Kasa, ya ƙara da cewa “Idan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, hukumomi da masana’antu masu zaman kansu za su hada kai, kudirin gwamnati zai samar da ayyukan ci gaban kasa na zahiri cikin ƙanƙanin lokaci,”

Tuni dai gwamnoni da masu ruwa da tsaki da suka sami halartar taron suka yaba da wannan matsayar da gwamnatin ta dauka
Inda suka ce za su bayar da duk wani goyon baya ga kwamitin shugaban kasar don ganin an samar da tsari mai kyau wajen rabon tallafin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *