Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun yada labarai, ya fitar a yau Asabar, an bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda a halin yanzu yake Saint Lucia bai yi wani sabon nadin mukami ba.

Sanarwar ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da labarai cewa an sauke Sanata Akume daga mukaminsa, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne da aka kirkira don cimma wata manufa.

Fadar Shugaban Ƙasar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan jita-jita da basu da tushe da makama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *