Harin Bama: Shugaban Tinubu ya bayar da umarnin tura ƙarin sojoji da jirage marasa matuka, domin murkushe ‘yan ta’adda

Harin Bama:
Shugaban Tinubu ya bayar da umarnin tura ƙarin sojoji da jirage marasa matuka, domin murkushe ‘yan ta’adda.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a wani sakon jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno kan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa yankin Darajamal da ke Karamar Hukumar Bama, harin, wanda aka kai a daren Juma’a, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da sojojin Najeriya.

Shettima Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar kafa ‘yan sandan jihohi domin tunkarar kalubalen tsaro a matakin farko.

Tuni gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci yankin da abin ya shafa a ranar Asabar domin jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.

Mataimakin Shugaban Kasar ya tabbatar wa da al’ummar jihar cewa za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatin tarayya a yakin da jahar ke yi da rashin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *