Harin sama na sojojin Najeriya ya hallaka gungun ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa bayan kai hari a Kano

Rundunar Haɗin Gwiwa (JTF) tare da goyon bayan sashen sama na Operation Fansan Yamma sun hallaka akalla ‘yan bindiga 23 da ke ƙoƙarin tserewa daga Jihar Kano bayan kai hare-hare a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.

Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Soja, Birgedi na 3 na Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Zubairu Babatunde, ya fitar a Kano ranar Lahadi, ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kaddamar da hare-haren ne a daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a.

Sanarwar ta ce dakarun ƙasa sun dakile hare-haren cikin nasara tare da yi wa maharan mummunar asara, kafin su bi sawun ‘yan bindigar da suka tsere zuwa ƙauyen Karaduwa a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

A cewar Babatunde, rahotannin leƙen asiri sun nuna cewa ‘yan bindigar sun taru a Dan Marke da ke Matazu domin binne wasu daga cikin ‘yan uwansu da aka kashe a yayin artabun da dakarun soji.

“Bangaren sama na Sector 2 Operation Fansan Yamma ya gano ‘yan bindigar tare da bibiyar motsinsu har sai da baburansu suka taru bayan sun ketare wani busasshen rafin ruwa,” in ji sanarwar. “Daga nan aka kai farmakin sama cikin kwarewa, wanda ya yi sanadin hallaka akalla ‘yan ta’adda 23, yayin da ake zargin wasu da dama sun jikkata.”

Sanarwar ta ƙara da cewa aikin, wanda ya samu goyon bayan ayyukan leƙen asiri na sama (ISR), ya kuma haifar da lalata makamai da kayan aiki da dama na ‘yan bindigar.

Kwamandan Birgedi na 3 na Rundunar Sojin Nijeriya ya yabawa sashen sama da dakarun ƙasa bisa jarumtaka da jajircewarsu a yayin aikin, yana mai cewa “jarumtaka da juriya da suka nuna abin a yaba ne.”

Babatunde ya tabbatar da cewa halin tsaro a Jihar Kano na nan cikin kwanciyar hankali, inda dakarun ke ci gaba da sintiri da sa ido a yankunan da abin ya shafa. Ya ce ƙwazon aiki da ƙwarin gwiwar dakarun na da matuƙar gamsarwa.

Rundunar Sojin Nijeriya ta gode wa al’umma kan goyon bayan da suke bayarwa a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da ta’addanci, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai cikin gaggawa. Ta jaddada cewa sojoji, tare da sauran hukumomin tsaro, za su ci gaba da ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da tabbatar da tsaron ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *