HATTARA DAI ‘YAN GIDOGA: CBN zai haramta wa masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar

Ashafa Murnai

Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai fito shirin ƙaƙaba wa masu rubuta cek da sunan biyan kuɗi ga wani, alhali ba su da isassun kuɗi a asusun bankin su hukuncin daina hulɗa da su a bankuna har tsawon shekaru biyar. takunkumin haramta cinikayya na shekaru 5 ga masu rubuta takardun bashi (cheque) na bogi

Ana wannan shirye-shiryen fara aiki da doka da ƙa’idojin kan masu rubuta cek na bogi, wanda a Turance ake kira ‘dud check’, a matsayin babban laifi a tsarin hada-hadar kuɗaɗe a bankuna.

CBN dai na shirin kafa wannan sabuwar doka da za ta hana masu maimaita rubuta cek na gidoga ci gaba da yin mu’amalar banki na tsawon shekara biyar.

A ƙarƙashin wannan ƙudirin doka, za a bayyana mutum a matsayin “mai rubuta cekin kuɗi na bogi sau da yawa”, idan ya rubuta takardun bashi sau uku kuma aka ƙi biyan su, saboda rashin isasshen kuɗi a asusun bankin sa.

CBN ta bayyana wannan a cikin daftarin ƙa’idojin da ta fitar cikin wannan mako, dangane da “Shirin Magance Rubuta Cek Na Bogi”, wanda ke bai wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi ikon sanya sunayen irin waɗannan mutane a jerin waɗanda banki ya yi nuni cewa ba a ba su amana.

Daga cikin abin da dokar za ta tanadar, an rattaba cewa waɗanda suka karya doka za a hana su karɓar lamuni, sannan a hana su samun lamuni daga kowanne banki.

Kuma za a hana su buɗe asusun ‘current account’ na tsawon shekaru biyar.

Bankuna kuma za su ƙwace ragowar littafin cekin kuɗaɗen da ke hannun sa da bai a amfani da su ba. Sannan a shigar da sunan sa da bayanan sa, a matsayin mai laifin da gangaci ne ci gaba da yin hulɗar banki da shi, wato ‘Credit Risk Management System’ (CRMS).

An tanadi takunkumi ga masu maimaita laifin, ta hanyar tsananta hukunci ga masu sake aikata laifi, inda aka tanadi cewa duk wani abokin ciniki da ya sake rubuta takardar bashi ta bogi, wato cek, bayan kammala hukuncin shekara biyar zai sake fuskantar kara wasu shekara biyar a duk lokacin da ya maimaita laifin.

Amma za a cire sunan sa daga wannan takunkumi idan lokacin hukuncin ya ƙare, ko kuma banki ya tabbatar an yi kuskuren shigar da sunan mutum.

Bankuna dole ne su sabunta bayanan mutum a cibiyoyin bayanan masu rubuta cek na gidoga, tare da sanar da shi a rubuce bayan ya ƙare wa’adin hukuncin.

Ƙudirin ya kuma tanadi hukunci kan bankunan da suka gaza aiwatar da ƙa’idojin, inda za su fuskanci tarar
Naira biliyan 5 idan ba su aiwatar da takunkumin ba.

Sai tarar Naira miliyan 3 idan suka buɗe ‘current account’, ba tare da binciken CRMS ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *