Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta sauka da kaso 22.22 cikin dari a watan Yuni 2025, daga 22.97% da aka samu a watan Mayu. Wannan rahoto ya fito ne daga sabon rahoton Hauhawar farashi “Inflation Report” da kuma rahoton farashin masu sayan kaya “Consumer Price Index (CPI)” da hukumar ta fitar a Abuja, wanda ke nuna ci gaban da aka samu a fannin tattalin arziki bayan sabunta ma’aunin kididdiga daga shekarar 2009 zuwa 2024.
Rahoton ya nuna cewa a bangaren hauhawar farashin abinci, an samu raguwar kashi 18.90 cikin dari daga shekarar da ta gabata, inda adadin ya sauka daga 40.87% a Yuni 2024 zuwa 21.97% a Yuni 2025.
Jihar Zamfara ce ta fi samun saukin hauhawar farashi da 9.90%, sai Yobe da 13.51% da Sokoto da 15.78%.
Hukumar NBS ta bayyana cewa sabunta tsarin kididdigar CPI da aka yi ya taimaka wajen dacewa da yanayin tattalin arzikin zamani. Babban Jami’in Kididdiga na Kasa, Adeyemi Adeniran, ya ce wannan sabuntawa na nufin inganta gano sahihin bayanai ta hanyar sabunta kayayyakin da ake amfani da su, da kuma karin wasu bangarorin kasuwa da hanyoyin tattara bayanai don a sami cikakken fasali na yadda tattalin arzikin kasa ke tafiya.