Daga Tanimu Yakubu
Jaridar Daily Trust ta ranar 6 ga Oktoba 2025, tana ɗauke da ra’ayin ta mai nuni da cewa “Shirin Shigo da Abinci da Gwamnatin Tinubu ke yi yana Gurgunta Harkokin Noma a Arewa.” Ra’ayin jaridar ya nuna damuwa kan makomar manoman Arewa da halin da za su tsinci kan su a ciki.
Ra’ayin na gidan jaridar ya yi nuni da matsi da takurar da manoman karkara ke fuskanta, kama daga tsadar noma, barazanar sauyin yanayi, matsalar tsaro da kuma fargabar gogayyar farashi da kayan abincin da ake shigo da su daga waje. Lallai kuwa akwai waɗannan ƙalubale, to amma duk Gwamantin Tarayya na sane da su, kuma tana taka-tsantsan da su.
Sai dai kuma cewa wai shigo da kayan abinci da gwamnati ke yi yana “gurgunta” harkokin noma a Arewa, jaridar ba ta gabatar da wasu hujjoji ba, ba ta kuma yi duba da la’akari da tsare-tsaren gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na game-garin faɗin ƙasar nan ba.
Gaskiyar shi wannan tsari dai an bijiro da shi ne hususan domin gaggauta samar wa jama’a sauƙin rayuwa a yayin da gwamnati ke aiwatar da tsare-tsaren farfaɗo da arzikin ƙasa mai dogon-zango.
Tilas Ta Sa Tinubu Gaggata Shigo da Abinci, Ba Watsi da Manoma Ya Yi Ba:
Nijeriya ta fuskanci matsanancin ƙarancin abinci a daidai tsakiyar 2025. Malejin tsadar abinci ya cilla sama, har sai da ya ƙaru da kashi 40 bisa 100. Sannan kuma nauyin aljihun jama’a ya ragu sosai, ba su iya sayen abincin da zai wadace su. Miliyoyin jama’a suka riƙa gaganiya da tsadar abinci a manyan biranen ƙasar nan da dama. Duk a lokacin, aka kuma fuskanci annobar ambaliya a Arewa-maso-gabas. Ga kuma fari ya addabi Arewa-maso-Yamma, sai kuma matsalar rashin tsaro da ta baibaye yankin Tsakiyar Nijeriya. Waɗannan matsaloli sun haifar da raguwar yawan amfanin gonar da manoma ke nomawa.
Dalilin waɗannan matsaloli ne Shugaban Ƙasa ya amince da jingine dokar karɓar kuɗaɗen haraji daga kayan abincin da ake shigowa da su, irin su masara, shinkafa, alkama, dawa da kuma gero. Amma hakan ba kaucewa aka yi kan shirin inganta harkokin noma ba. An dai shigo da kayan abinci ne domin kauce wa ɓarkewar yunwa, saisaita farashin kayan abinci daidai aljihun talakawa, sannan kuma a dawo wa jama’a da yaƙinin kyakkyawar fatan da suke da shi kan gwamnati.
Da Tinubu bai gaggauta bayar da umarnin cire harajin shigo da waɗannan kayan abinci ba, to tabbas sai gwamnati ta riƙa kamfatar maƙudan kuɗaɗe tana biyan tallafin kayan abinci, ko a gaggauta shigo da kayan abinci da kuɗaɗen da ba su cikin kasafin kuɗaɗe. Da an yi hakan kuwa, to lallai sai an fuskanci mummunan tsadar kayayyaki, sannan kuma a haifar da wawakeken giɓin kasafin kuɗaɗe. Saboda haka abin da aka yi hanya ce mai kyau da aka sauƙaƙa wa magidanta tsadar rayuwa, ba tare da haifar da tangarɗa kan tattalin arzikin ƙasa ba.
Yadda Gwamnati Ke Farfaɗo da Harkar Noma Yayin da Take Sassauta Farashin Abinci:
Tunanin bijiro da ɗaukin gaggawa wajen shigo da abinci domin sauƙaƙa farashi, ya zo ne tare matakan bunƙasa yawan abincin da ake nomawa:
- Shirin Samar da Kayan Aikin Noma, wato Agricultural Inputs Support Window (AISW): Samar da Naira biliyan 150 ta Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya tare da Babban Bankin Nijeriya (CBN), domin rage farashin takin zamani da magungunan ƙwari zuwa sauƙin kashi 22 na farashin su. Sai kuma tallafa wa ƙungiyoyi da sassaucin kuɗin safarar kayayyaki.
- Faɗaɗa Filayen Noma:
Ma’aikatar Samar Ruwa ta Tarayya ta fara aikin faɗaɗa filayen noma har faɗin eka 400,000 a Haɗejia, Bakolori da Daɗin Kowa. waɗannan ayyuka ana ci gaba da gaggauta yin su domin a bunƙasa noman rani a 2026. - Rumbunan Tanadin Abinci da Sassauta Farashi: Ana samar da manyan rumbunan adana abinci har zuwa tan 750,000, waɗanda za a fitar da su kasuwanni a lokacin rani, ta yadda za a daidaita farashin kayan gona, ba tare da an dagula darajar amfanin gona ba.
- Tsarin Bayar Da Lamuni da Raba Asara a ƙarƙashin ACGSF a yanzu zai yi fa’ida sosai ga ƙananan manoma, tare da samun tabbacin sa’ida daga Gwamnatin Tarayya a yayin da aka fuskanci asara sakamakon matsalar tsaro ko ambaliya.
- Shirin Dawo da Harajin Shigo da Kayan Abinci: Dakatar harajin kayan abinci abu ne mai taƙaitaccen lokaci, nan da watan Disamba 2025. Cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 ne kuma za a dawo da ƙaramin harajin kayan abinci, idan aka samu cigba a fannin samar da abinci.
Waɗannan matakai sun nuna tare da tabbatar da cewa tsarin da wannan gwamnati ke amfani da shi wajen bunƙasa kayan abinci, ba a gina shi kan shigo da abinci kaɗai ba. An gina shi ne kan tunanin samar da sassaucin tsadar rayuwa, domin kaiwa ga iya dogaro da kai.
Saisaita Tunanin Masu Mummunar Fahimta:
Ra’ayin jaridar Daily Trust ya yi shaci-faɗin cewa ɗage biyan harajin shigo da kayan abinci da aka yi na wani lokaci, wai ya gurgunta manoman Arewa. Wannan kintace ne kawai, jaridar ba ta yi la’akari da cewa shi kan sa tattalin arzikin ya fuskanci tsadar musayar kuɗaɗen waje, matsalar wutar lantarki da sauran matsaloli, waɗanda suka haifar da cikas ga samun riba, tun ma kafin a dakatar da karɓar harajin shigo da kayan abinci daga waje.
Maganar gaskiya tsarin shigo da abinci da aka yi, ya amfani masu samar da abinci a cikin ƙasa, domin ya daƙile hauhawar farashi, ya kawar da mummunar ɗabi’ar ɓoye abinci a fito da shi lokacin da ya yi tsada, kuma ya tabbatar da samun kayan aikin noma daidai gwargwadon ƙarfin aljihun manoma, sai kuma samar da kayan masarufi ta yadda sauƙin sa ya sa bai yi ƙaranci ba. Matsawar aka daƙile hauhawar farashin kayan abinci, to manoma za su iya tsara yadda za su yi noma da cin moriyar sa, ba tare da shakku ba.
Kuma yana da muhimmanci a sani cewa tsarin samar da abinci a Nijeriya yana da alaƙa tsakanin wannan yanki da sauran kowane yankin ƙasa. Adadin amfanin gonar da ake buƙata a birane da garuruwa na da tasiri ga kasuwannin yankunan karkara, yayin da sauƙaƙa farashi, zai kawar da yunƙurin tayar da tarzoma. Kuma zai zama kandagarkin kare nauyin aljihun miliyoyin marasa ƙarfi.
Fa’idoji da Alfanun Ɗage Harajin Shigo da Abinci:
Ci Gaba da Ƙarfafa Manoma da Kare Masu Sayen Kayan Abinci:
Yayin da ake ci gaba da samun haske, Gwamnatin Tarayya za ta dawo da harajin shigo da kayan abinci tare da faɗaɗa tsarin sarrafa amfanin gona, adana kayan gona da kuma safarar sa. Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya na aiki tare da Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, Babban Bankin Nijeriya, CBN da Majalisar Tattalin Arziki domin tabbatar da cewa kuɗaɗen yin manyan ayyukan inganta tattalin arziki irin su gina titina a yankunan karkara, samar da masana’antun takin zamani da rumbunan tanadin hatsi duk an ba su fifiko a jihohin arewa.
Burin da ake so a cimma a nan, shi ne bayar da dama yadda manoman Arewa za su riƙa gogayya da na Kudu ta ɓangaren yawan albarkar noma, samun lamuni da kuma samar da kayayyakin inganta rayuwa da ƙasa baki ɗaya.
A ƙarshe, a yi wa shirin shigo da abinci daga waje da Shugaba Tinubu ya bijiro da shi kyakkyawar fahimta cewa shiri ne na gaggawar magance matsalar abinci da ta kunno kai, domin hana ta yi muni. Amma ba an yi don a dagula ko gurgunta kasuwar kayan abinci ba. Yunƙuri aka yi mai tabbatar da kyakkyawan jagorancin nuna tausayi ga marasa galihu.
Yayin da komai ke ƙara ɗaukar saiti sannan tsadar kayayyaki na ci gaba da lafawa nan zuwa watan Disamba 2025, Nijeriya za ta fara tafiya bisa cikakkar turbar samar da wadataccen abinci a cikin gida. Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya na jaddada ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke kan yi wajen bunƙasa harkokin noma a Arewa, a matsayin yankin wanda da shi ne jagoran samar da wadataccen abinci ga ƙasa, sannan kuma ya kasance yanki mai yalwar arziki.
Saboda haka a daina fassara wannan shirin shigo da abinci na wucin-gadi a matsayin kauce wa tsarin da ake a kai. A’a, hanya ce ta gaggauta farfaɗowa – kuma ana tafiya ɗoɗar kan turbar shirin farfaɗo da noma a Nijeriya.
*Yakubu shi ne Babban Darakta, Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya,
Fadar Shugaban Ƙasa,
Abuja.
