Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da Kasafin Kuɗin Tarayya na shekarar 2026 a gaban zaman haɗin gwiwar Majalisar Tarayya, inda ya bayyana cewa kasafin ya mayar da hankali kan ƙarfafa tsaro, bunƙasa tattalin arziki, inganta jin daɗin al’umma da gina ƙasa mai ɗorewa.
Kasafin, mai taken “Kasafin Ƙarfafa Tushen Arziki, Sabunta Juriya da SAMAR da Cigaba ga Kowa”, ya nuna aniyar gwamnati na ƙarfafa nasarorin da aka samu a cikin shekaru biyu da rabi na gyare-gyaren tattalin arziki, tare da tabbatar da cewa cigaban da ake samu ya shafi rayuwar talakawa kai tsaye.
Tsaro da Kare Ƙasa
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, inda aka ware naira tiriliyan 5.41 domin harkokin tsaro da kare ƙasa. Ya ce za a mayar da hankali kan ƙarfafa rundunonin soji, inganta leƙen asiri, tsaron iyakoki da amfani da fasahar zamani wajen sa ido.
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ba wajen yaki da ta’addanci, ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka masu tada hankali, inda duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai ba tare da izinin gwamnati ba za a ɗauke ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
Lafiya
A fannin lafiya, shugaban ya bayyana cewa an ware naira tiriliyan 2.48, wato kusan kashi 6 cikin 100 na kasafin baki ɗaya, domin inganta asibitoci, kayan aiki da kula da lafiyar jama’a. Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwa da gwamnatin Amurka ya buɗe hanyar samun dala miliyan 500 domin ayyukan lafiya a faɗin ƙasar, wanda zai taimaka wajen rage radadi ga marasa galihu.
Noma da Samar da Abinci
Tinubu ya jaddada cewa wadatar abinci na daga cikin manyan manufofin kasafin 2026. Ya ce gwamnati za ta zuba jari a tallafin kayan noma, injina, ban-ruwa, ajiyar amfanin gona da sarrafa shi, domin rage asara bayan girbi da ƙara kuɗin shiga ga manoma.
Ya bayyana cewa Bankin Noma zai jagoranci wani shiri da zai bai wa manoma damar noma hekta miliyan ɗaya, tare da samar da dubban ayyukan yi da kuma bunƙasa fitar da kayan noma zuwa ƙasashen waje.
Ilimi
A bangaren ilimi, kasafin ya ware naira tiriliyan 3.52, inda aka mayar da hankali kan faɗaɗa damar shiga manyan makarantu. Shugaban ya bayyana cewa asusun rancen karatu na NELFUND ya riga ya tallafa wa sama da dalibai dubu 788 a fadin manyan makarantu 229, lamarin da ke rage nauyin karatu ga iyaye da dalibai.
Ababen More Rayuwa da Tattalin Arziki
An ware naira tiriliyan 3.56 domin ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi, makamashi, tashoshin jiragen ruwa da ayyukan da ke jan jari daga masu zaman kansu. Shugaban ya ce ba tare da hanyoyi, wutar lantarki da sufuri ba, ba za a samu ayyukan yi ko bunƙasar kasuwanci ba.
Manufofi da Alkibla
Tinubu ya bayyana cewa kasafin 2026 ya ta’allaka ne kan manyan manufofi guda huɗu: ƙarfafa tattalin arziki, inganta yanayin kasuwanci, samar da ayyukan yi da rage talauci, da kuma kare marasa ƙarfi a cikin al’umma.
A ƙarshe, shugaban ya buƙaci Majalisar Dokoki da ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su ba da haɗin kai domin aiwatar da kasafin yadda ya dace, yana mai cewa, “Muhimmin kasafi ba shi ne wanda aka sanar ba, sai wanda aka aiwatar.”
Kasafin na 2026, a cewarsa, zai zama ginshiƙi wajen kai Najeriya ga tsaro, wadatar abinci, ingantacciyar lafiya, ilimi mai amfani da tattalin arziki mai ɗorewa, bisa tafarkin Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda).
