Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yaba wa Shugaba Tinubu, ta bukaci karin kulawa ga Arewa

Babban jigo a kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), kuma Wazirin Dutse, Alhaji Dr. Bashir Dalhatu, ya bayyana gamsuwa da wasu manyan matakai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka tun bayan hawansa mulki, musamman a fannin bunkasa tattalin arziki da wanzar da zaman lafiya a kasashen ECOWAS.

Yayin da yake jawabi a wurin zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma da aka shirya a Kaduna karkashin Ahmadu Bello Memorial Foundation, ya bayyana cewa kirkirar Ma’aikatar Kiwon Dabbobi da bude kan iyakoki sun kawo sauki ga rayuwar al’ummar Arewa.

Dalhatu ya yabawa Shugaban kasa kan yadda ya ke tura kudade da dama zuwa jihohi don tallafawa ci gaban jama’a, musamman a yankin Arewa. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yadda Shugaba Tinubu ya sauya salon shugabanci da aka saba, inda ya nuna cikakken kwazo wajen dakile yunkurin rikici a yankin ECOWAS.

“Shugaban kasa ya taka rawar gani, ya cancanci yabo, kuma muna godiya da irin saukin rayuwa da ake samu yanzu a Arewa sakamakon wadannan matakai.”

Wazirin Dutse ya kuma jaddada cewa akwai sauran rina a kaba, inda ya lissafa wasu manyan bukatu da Arewa ke da su wanda har yanzu ba a cika su ba. Ya ce ACF ta kai bukatunta ga Shugaba Tinubu tun ranar 30 ga Mayu, 2024, ciki har da batun rashin tsaro, talauci, yara marasa zuwa makaranta, da batutuwan manyan ayyuka kamar Ajaokuta, Mahakar mai ta Kolmani, da gina hanyoyi a Arewa. Ya bukaci a kafa kwamiti da zai ci gaba da duba wadannan batutuwa, kamar yadda Shugaban kasa ya amince.

Dr. Bashir Dalhatu ya bukaci gwamnati ta dauki Arewa a matsayin abokiyar tafiya mai mahimmanci ba kawai a lokacin neman kuri’a ba. Ya ce akwai bukatar gyara tsarin kasafin kudi da samar da masana’antun noma a Arewa don tallafawa manoma da samar da ayyukan yi.

Ya kuma bayyana godiyar sa da halartar manyan wakilan gwamnati da suka zama kunnuwan Shugaban kasa a wajen taron, tare da jaddada kwarin gwiwar da suke da shi akan gwamnati da kuma kyakyawan zaton za a cika wa arewa dukkan muradun ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *