Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma da Makiyaya — Jega

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aniyar ta ta bunƙasa harkar kiwon dabbobi a Nijeriya a matsayin wata muhimmiyar hanya ta magance rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, tare da amfani da damar tattalin arzikin da ke cikin ɓangaren.

Ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Harkar Kiwo, Farfesa Attahiru Jega, shi ne ya bayyana hakan a wurin taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, wanda Gidauniyar Sa Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, a ranar Laraba.

Jega ya bayyana cewa sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo tana ɗaya daga cikin ginshiƙan da ke cikin shirin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na sauya fasalin ɓangaren kiwon dabbobi.

Ya jaddada cewa ana aiwatar da hangen nesa na Shugaban Ƙasa ba tare da son rai na siyasa ba, tare da mayar da hankali kan haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya, al’ummomin makiyaya da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *