Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Alhaji Ɗanlami Nmodu murna kan zaɓen sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar Gizo (GOCOP) a zaɓen da aka gudanar a Legas.
Idris ya ce: “Malam Nmodu, mawallafin Newsdiary Online, wanda nake da alaƙa ta abota da ta aiki da shi tsawon shekaru da dama, ɗan jarida ne nagari wanda ya tabbatar da cancantar sa a aikin jarida, kuma ya dace da wannan matsayi mai daraja.”
Ministan ya kuma yaba wa tsohuwar Shugabar GOCOP, Hajiya Maureen Chigbo, mawallafiyar RealNews Online, kan jagorancin ta na mawallafan onlayin su sama da ɗari da kuma barin “gado mai cike da daraja, ƙima, gaskiya, da cigaba mai ban-sha’awa ga ƙungiyar.”
Idris ya yi kira ga sabon Shugaban na GOCOP da abokan aikin sa na gudanarwa da su bai wa haɗin kan ƙungiyar muhimmanci, inda ya jaddada muhimmancin ƙulla kyakkyawar dangantaka a ƙungiya wadda za ta dauwama tsawon lokaci.
Ya ce: “Yayin da nake taya Nmodu murna, yana da kyau in yi kira a gare shi da ya jagoranci ƙungiyar ta hanyar haɗa kai, wanda ke tabbatar da cewa dukkan membobin GOCOP sun haɗa hannu da hannu wajen ci gaba da cimma burin ƙungiyar.”
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin lura da “mummunan tasirin labaran ƙarya, bayanan da ba daidai ba da kuma labaran ɓarna da ke barazana ga sahihancin aikin jarida.”
Saboda haka, Idris ya yi kira ga sabon shugabannin GOCOP da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, wadda ke jagorantar wayar da kan jama’a kan ilimin kafofin yaɗa labarai a faɗin ƙasar nan.
“Na yarda da Malam Nmodu, wanda ya gina sana’ar aikin jarida bisa gaskiya, jajircewa, ƙarfin hali, da juriyar aiki, ya kuma kawo wannan irin ƙwarewa wajen haɗin gwiwa da gwamnati domin tabbatar da aminci da ilimin kafofin watsa labarai, musamman a cikin harkar kafofin watsa labarai na gidan gizo,” inji shi.