Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye mukaminsa nan take, bisa dalilai na lafiya.
A cikin wata wasika da aka rubuta ranar 1 ga Disamba zuwa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Badaru ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa daga kujerar minista ne domin mayar da hankali kan lafiyarsa.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa, tare da gode masa bisa gudunmawar da ya bayar wa ƙasar tun bayan nadin da aka yi masa a ranar 21 ga Agusta 2023.
Daga cikin bayanan da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Shugaba Tinubu zai tura sunan wanda zai maye gurbin Badaru zuwa majalisar dattawa a cikin wannan makon.
Badaru Abubakar, wanda ya kai shekara 63, ya shugabanci jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu daga 2015 zuwa 2023, kafin nadinsa a matsayin Ministan Tsaro.
