Ministan Yaɗa Labarai Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da kamfen na wayar da kan ɗaliban makarantun sakandare kan kafofin sadarwa da yadda ake amfani da su ta hanyar da ta dace.

Da yake jawabi a taron TEDxNTICAbujaYouth 2025 da aka gudanar a makarantar Nigerian Tulip International College, Abuja, a ranar Asabar, ministan ya jaddada yadda kafafen sada zumunta suke da tasiri ga matasa, tare da buƙatar koya masu dabarun tantance sahihancin bayanan da suke karantawa da watsawa a intanet.

Ya ce: “Saboda ina cikin harkar sadarwa, na kasance mai matuƙar sha’awar yadda mutane suke yaɗa labarai, da yadda mutane za su iya sadar da juna cikin ɗan lokaci kaɗan daga ko’ina cikin duniya, sannan kafin mu ankara sai ga sararin sadarwar dijital ya buɗe. Yanzu akwai Instagram, Facebook, WhatsApp, X da sauran su, amma kuma wannan ma wani ƙalubale ne. Yanzu sadarwa maimakon ta zama abin haɗin kai, tana iya zama abin da za a yi amfani da ta ta hanya mara kyau.”

Ya ƙara da cewa, “Haɓakar duniyar dijital ita ma ta kawo zamanin yaɗa labaran ƙarya, da ruɗani da yaɗa bayanan da ba su da tushe.”

Da yake magana kan jigon taron mai taken “Shauƙi”, Idris ya ba da tarihin rayuwar sa, inda ya bayyana irin shauƙin da ya ke da shi tun yana matashi wajen zama ɗan jaridar gidan rediyo ko talbijin, sai dai wata matsala a gidan su ta tilasta masa shiga jami’a kafin ya cimma burin sa.

Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya.

“Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo ya amfanar.”

Ya ce kafin ya zama minista, ya mallaki tashar rediyo da talbijin har ma da gidan jarida.

Ministan ya buƙaci matasa da kada su yi watsi da burin su ko da ba sa ganin damar cimma buƙatar su. Ya ce shauƙin sa ne yake motsa shi wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar ƙarfafa fahimtar kafofin sadarwa.

Idris ya kuma bayyana cewa daga watan Nuwamba mai zuwa, Nijeriya za ta fara gudanar da Cibiyar Ilimin Kafofin Sadarwa ta UNESCO mai Mataki na 2.

Ya ce: “Ni ne na jagoranci Nijeriya wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Sadarwa ta UNESCO Category 2 – wadda ita ce irin ta ta farko a duniya – kuma za a kafa ta a Abuja. Zuwa watan Nuwamba idan hukumar UNESCO ta bayar da amincewar ƙarshe, duk duniya za ta dinga kallon Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa, “Don haka ba wai kawai ku matasa maza da mata ku ɗauki makirfo, kwamfuta ko wayoyin ku na zamani ku fara faɗin duk abin da kuka ga dama ba ne. Kuna iya samun ilimi, amma kuma kuna buƙatar fahimtar yadda kafofin sadarwa suke.”

An tsara cibiyar ne don koyar da matasa daga Nijeriya da ƙasashen waje dabarun amfani da kafofin sadarwa cikin basira tare da yin kaffa-kaffa da kuma kare kan su daga labaran ƙarya da yaɗuwar bayanan da ba su da tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *