Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a matsayin sa na Shugaban Ƙungiyar Cigaban Jihar Neja (Niger State Development Forum – NSDF) ya jagoranci taron ƙungiyar a ofishin sa dake Abuja, a jiya Talata, tare da mataimakin ƙungiyar, ƙaramin Ministan Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci, Sanata Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, da sauran mambobin ƙungiyar.
Ministan ya jaddada cewa, kamar yadda ya yi alkawari tun lokacin da aka kaddamar da sabon kwamitin gudanarwa na ƙungiyar a farkon wannan shekara, zai ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa wannan ƙungiya ta ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban jihar Neja.