Muhimmin lokaci a Nijeriya: Hujjar da ta sa hanyar da aka ɗauka ita ce mai ɓullewa

Daga Mohammed Idris

Yayin da muka shigo sabuwar shekara, tambayoyin da ake ta yi a kasuwannin mu, gidajen mu da wuraren ayyukan mu a bayyane suke kuma suna da matuƙar muhimmanci. Tambayoyi ne da mutane ke yi dangane da farashin abinci, tsaro a al’ummomin mu, da kuma alƙiblar da ƙasar mu take fuskanta. Wajibi ne ga wannan ma’aikata tamu—wato Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai—ta yi magana kai-tsaye kan waɗannan batutuwa, ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba, kuma cikin girmamawa ga kowane ɗan Nijeriya da ke ɗauke da nauyin wannan lokaci.

Watanni talatin da ɗaya da suka gabata sun kasance na sauye-sauye na asali, kuma galibi masu wahala. Gyare-gyaren da muka kawo masu ƙwazo—waɗanda suka fara da shirye-shirye masu raɗaɗi amma na dole, musamman ma dai cire tallafin man fetur da gyara farashin musayar kuɗi—an tsara su ne domin karya daɗaɗɗiyar durƙushewar da tattalin arzikin ƙasar nan ya yi tare da tabbatar da samun makoma mai ɗorewar wadata. Ba a taɓa yi mana alƙawarin cewa wannan hanya za ta kasance mai sauƙi ba, amma an yi alƙawarin za ta kasance cikin gaskiya tare da kyakkyawar manufa.

A yau, alamun farko na waccan kwanciyar hankali da aka yi alƙawari sun fara bayyana. Disambar 2025 ta nuna watanni goma sha uku a jere na bunƙasar harkokin kasuwanci. Kamfanonin ƙasashen waje suna sake kallon Nijeriya da cikakkiyar niyya. Kuɗin GDP ɗin mu suna ƙaruwa, hauhawar farashi tana raguwa, kuɗin ajiyar mu a ƙasar waje suna ƙaruwa. Waɗannan ba ƙididdiga na rahotanni kawai ba ne; su ne tubalan da ake gina ingantacciyar rayuwar yau da kullum da su.

Sai dai ba a mulkar ƙasa da alƙaluma kaɗai. Ana mulkin ƙasa ne ta hanyar riƙe amana—amana da ake gina ta ta hanyar bayyanannen bayani game da ƙalubale da kuma cigaba. Rawar da nake takawa ita ce zama muryar da ke daidaito ga wannan gwamnati, in bayyana manufofin mu da ayyukan mu.

A kan wannan kwanciyar hankalin tattalin arziki da ke fitowa, mun ba da fifiko ga shirin shiga kai-tsaye da ke taɓa rayuwa. Shirin ba da rance ga ɗalibai (NELFUND) yana buɗe ƙofofi. Shirin iskar gas (CNG) na Shugaban Ƙasa yana nufin rage kuɗin sufuri. Shirye-shirye irin su LEEP, Jubilee Fellows, da 3MTT an tsara su ne domin bai wa matasan mu ƙwarewa da dama kai-tsaye. A harkar noma, an sake zuba jari mai tarihi ga Bankin Manoma, tare da sababbin tanade-tanaden samar da injina domin yaƙar ƙarancin abinci tun daga tushe.

Haka kuma muna gudanar da manyan ayyukan more rayuwa. Hanyar Gaɓar Teku, titin Sakkwato zuwa Badagiri, bututun iskar gas na AKK, da sababbin layukan dogo—duk domin haɗa tattalin arzikin mu da rage tsadar da yanayin ƙasar mu yake haifarwa.

A fannin tsaro, ana aiwatar da sabon tsari. Muna zuba jari sosai wajen ɗaukar jami’ai aiki, samar da kayan aiki, da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa domin murƙushe ta’addanci da fashi da makami. Ceto ɗaliban mu da aka sace a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan shaida ce ta wannan jajircewa, kuma za mu ci gaba har sai kowane ɗan Nijeriya ya samu tsaro.

Na fahimci gajiyar da ke zuwa tare da juriya. Damuwa kan farashi, fargabar lafiyar abokan zama, da burin ganin sakamako cikin gaggawa—duk waɗannan yanaye-yanaye ne na ɗan’adam kuma suna cikin yanayin shugabanci. Wannan gwamnati tana sauraren ku. Ƙudirin mu shi ne mu hanzarta yarda da cewa waɗannan gyare-gyare za su koma sauƙi na zahiri da ya shafi jama’a da yawa.

Shi ya sa a cikin 2026, kasafi mai taken “Kasafin Kuɗin Ƙarfafa Ƙasa, Sabuwar Juriyar Zuciya da Wadata ta Bai-Ɗaya”, ya zama muhimmi. Alƙawari ne na ƙara ninka abin da yake aiki, da ƙarfafa nasarori, da tabbatar da cewa wadata ta bai-ɗaya da muke magana a kai ta zama gaskiyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya da yawa, cikin sauri.

Amma gina ƙasa alƙawari ne na juna. Mu a gwamnati mun ɗauki alƙawarin gudanar da jagoranci mai tsafta, da rarraba albarkatu cikin gaskiya, da yin bayanai a kai a kai. Mun yi alƙawarin fuskantar jama’a, bayar da hisabi kan amana, da bayyana hanyar da muke bi. A madadin haka, ƙarfin al’umma—shirye-shiryen mu na biyan haraji, kare dukiyar jama’a, shiga muhawara cikin gina kai, da ƙin rarrabuwar kawuna da yaɗa ƙarya—shi ne zai tabbatar da makomar mu baki ɗaya.

Wannan ma’aikata, a ƙarƙashin kulawa ta, za ta kasance mai gudanar da aiki tsakani da Allah da kuma kyakkyawar manufa. Za ta ci gaba da zama hanya mai tsare gaskiya, mai sauƙin samu, kuma mai kamanta gaskiya tsakanin gwamnati da ku jama’a. Za mu yi bayani, za mu kare, za mu saurara, kuma za mu bayar da rahoto. Za ku ci gaba da gani da ji daga wannan ma’aikata—murya bayyananniya ta aiki fisabilillahi kan dukkan ajandar gwamnati.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ba mutum ba ne wanda matsaloli ko ƙalubale suke firgita shi. Tsarin sa a kowane lokaci ya kasance cikin natsuwa da yanke shawara—yana mayar da ƙalubale wata dama don yin abubuwa mafi kyau da inganci. Hulɗoɗin mu na baya-bayan nan da Amurka shaida ne. A ƙarƙashin jagorancin sa, mun mayar da wani lokaci mai cike da tashin hankali wata dama ta ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu da kuma ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Duk da haka, duk da yake mun yi amanna da nasarorin da muka samu, ba mu son rayuwa koma-baya. Idanun mu suna kallon abin da ke gaba ne da yadda gobe za ta fi yau. A gare mu, kowane lokaci a yanzu dama ce ta ƙara ƙarfafa abin da ke aiki, domin mu girbe cikakken amfanin gyare-gyare.

Hanyar da ke gaba tana buƙatar haƙuri na kowa da ƙudirin zuciya na bai-ɗaya. Siyasar rarrabuwar kai da hayaniya za ta ci gaba da wanzuwa, to amma wahalar aikin gina Nijeriya da ke aiki ga kowa dole ta yi nasara. Mun shimfiɗa sabon tushe. Yanzu, dole ne mu gina gidan tare.

Ina yi wa kowane ɗan Nijeriya fatar shekara mai cike da zaman lafiya da aiki mai albarka.

Mohammed Idris, fnipr,
Mai Girma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *