Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa asusun tallafi na Naira Biliyan 200 domin taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa (MSMEs) wajen ƙarfafa musu da magance matsalolin da ke hana su ci gaba.
Tinubu ya bayyana haka ne a Abuja ranar Litinin yayin da ya buɗe taron tattalin arziki na ƙasa (NESG) karo na 31, inda ya ce, bayan nasarar da Najeriya ta samu na bunƙasar tattalin arziki da ya kai kashi 4.23 cikin 100 a watan Satumba 2025, sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa a fannoni da dama.
Shugaba Tinubu wanda Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana cewa, dukkan matakan tattalin arzikin da ake ɗauka a gwamnatin Tinubu “ana yin su ne da niyyar daidaita bukatun jama’a da ka’idar tattalin arziki.”
Shugaban ƙasan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa matasa, marasa aikin yi, da masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma, ta hanyar samar da hanyoyin samun rancen kudi, tallafi da jarin hadin gwiwa domin bunkasa sana’o’i da kirkire-kirkire.
Ya ce, “A matsayina na shugaba a gwamnati mai kishin jama’a, burinmu shi ne dawo da kwarin gwiwa ga masu ƙaramin ƙarfi da marasa aikin yi. Mun samar da hanyoyi domin matasanmu su iya samun tallafin kudi har zuwa dalar Amurka 100,000 domin faɗaɗa kasuwancinsu da ƙirƙirar sabbin hanyoyin samun abin dogaro.”
Tinubu ya kara da cewa, “Mun kafa asusun tallafi na Naira Biliyan 200 domin taimakawa ƙananan masana’antu da ‘yan kasuwa.”
Shugaban ƙasan ya danganta daidaituwar tattalin arzikin ƙasa da aka samu da haƙuri da sadaukarwar ‘yan Najeriya bayan cire tallafin mai da sake fasalin kasuwar kudaden waje.
Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru zuwa Naira Tiriliyan 372.8 a 2024 daga Naira Tiriliyan 309.5 a 2023, inda harajin da gwamnati ke samu ya karu sosai, yayin da yawan kuɗin shiga ya haura Naira Tiriliyan 27.8 a watan Agusta 2025, wanda ya zarce abin da aka yi hasashe.
Haka kuma, shugaban ƙasan ya bayyana cewa an rage yawan bashin da ake biya daga kashi 97 cikin 100 zuwa kasa da 50 cikin 100, lamarin da ya sa Fitch da Moody’s suka ɗaga matsayin bashin Najeriya zuwa matakin “B” da “B3”.
Ya ƙara da cewa, harajin da ake tarawa a yanzu ya kai kashi 13.5 cikin 100 na GDP, sabanin ƙasa da kashi 7 cikin 100 da ake samu a baya, yayin da bashin Najeriya ke kashi 38.8 cikin 100 na GDP, ƙasa da iyakar da dokokin ƙasa da ECOWAS da Bankin Duniya suka kayyade.
Tinubu ya ce an ƙara yawan kuɗaɗen da ake rarrabawa ga jihohi don su gudanar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen jin ƙai, yana mai jaddada cewa nasarar tsarin ya dogara ne akan ba wa kowace jiha ikon yin abubuwan ci gaba daga albarkatun da take da su.
Ya kuma tabbatar da cewa dokokin haraji guda huɗu da ya rattaba hannu a baya-bayan nan za su taimaka wajen ƙara samun kuɗin shiga, rage dogaro da mai, da sauƙaƙa bin doka wajen biyan haraji.
A nasa jawabin, Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya yabawa haɗin gwiwar ma’aikatarsa da NESG, yana mai cewa haɗin gwiwar ya samar da kyakkyawan alaƙa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu wajen bunkasa tattalin arzikin ƙasa.
Wadanda suka halarci taron sun haɗa da Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Mr. Wale Edun, Ministar Masana’antu, Dr Jumoke Oduwole, Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Yanar Gizo, Mr Bosun Tijjani.