Najeriya a yanzu ta wuce lokacin rashin daidaituwar tattalin arziki — Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tabbatar wa da masu zuba jari cewa yanzu ne lokacin da ya fi dacewa su zuba jari a Najeriya, domin ƙasar ta fice daga halin rashin daidaiton tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne a wajen taron ‘Bauchi Investment Summit 2025’, inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawar da manyan cikas da suka hana ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Shettima ya bayyana cewa, a yanzu kudaden da ake kashewa wajen biyan bashi sun sauka zuwa ƙasa da kashi 50 cikin ɗari daga sama da kashi 100, yayin da tattalin arzikin ƙasar (GDP) ya karu zuwa kashi 4.23 cikin ɗari.

Sanata Shettima ya ce an samu ƙaruwa mai yawa a fannin haraji da kudaden shiga da ba na mai ba, wanda ya tashi da kashi 411 cikin ɗari cikin shekara guda. Ya ƙara da cewa ajiyar kudin ƙasar a ƙasashen waje ya kai dala biliyan 43 a watan Satumba 2025, yana mai cewa, “Najeriya ta fita daga halin rashin tabbas, don haka yanzu ne lokacin da ya fi dacewa masu zuba jari su zabi Najeriya.”

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta dauki matakan cire tallafin mai da daidaita tsarin musayar kuɗi domin samar da dawwamammen ci gaba da kwanciyar hankali a harkokin tattalin arziki.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa halartar taron tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron. Haka kuma, Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya yi kira ga gwamnoni da shugabanni na Arewa da su mayar da hankali wajen aiwatar da sakamakon irin waɗannan taruka, yana mai cewa Arewa na da isassun albarkatu da za su iya fitar da yankin daga matsalolin tattalin arziki idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.
[09/10, 15:51] +234 706 474 1010: Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Na Jagorantar Taron Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a Abuja

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar zaman Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja. Zaman ya fara ne da ƙarfe 2:39 na rana a yau Alhamis, jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa ya kammala taron Majalisar Ƙoli ta Ƙasa inda ya gabatar da sunan wanda zai aka zaba a matsayin sabon shugaban INEC.

Taron ya zo ne makonni biyar bayan da Shugaban Ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana nazarin batun kafa rundunar ‘yan sanda na jihohi, tare da ƙarfafa sabbin jami’an tsaron daji (forest guards) da aka tura cikin dazuzzuka domin yaki da matsalar tsaro. A ranar 2 ga Satumba, 2025, yayin da ya karɓi tawagar jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Radda, Shugaba Tinubu ya ce: “Ina duba dukkan fannoni na tsaro; dole ne in samar da rundunar ‘yan sanda ta jihohi.”

A yayin zaman na yau, mahalarta sun yi addu’a domin tunawa da tsohon Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar 31 ga Agusta, 2025. Majalisar ta yi nazari kan kalubalen tsaro na yanzu, cigaban da aka samu a gyaran da akai a hukumar ‘yan sanda, da kuma harkokin jin daɗi da albarkatun jami’ai a fadin ƙasar. Haka kuma, ana sa ran za a tattauna batutuwa da suka shafi shugabanci da tsarin aiki tsakanin jihohi.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Sakataren Gwamnatin Ƙasa George Akume, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ibrahim Gaidam na cikin mahalarta zaman, tare da dukkan gwamnonin jihohi da wakilan su. Majalisar ‘Yan Sanda, wacce kundin tsarin mulki ya kafa ƙarƙashin sashe na 153, tana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, kuma tana ba da shawara kan tsari, gudanarwa da kula da rundunar ‘yan sanda, har ma da batun nada ko cire Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *