Najeriya da Amurka Sun Kai Harin Hadin Gwiwa Kan Manyan Maboyar ’Yan Ta’adda a Arewa Maso Yamma

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da hadin gwiwar tsaro da kasashen duniya musamman Amurka domin dakile barazanar ta’addanci a kasar. Wannan mataki, a cewar ma’aikatar, ya haifar da samun karin nasarori a yunkurin kai hare-haren jiragen sama da suka yi a wasu sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar dauke da sa hannun Mataimakin Kakakin Ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, an bayyana cewa hadin gwiwar tsaron ya kunshi musayar bayanan sirri, dabarun tsaro, da sauran nau’ikan goyon baya da suka dace da ka’idojin kasa da kasa tare da mutunta ikon kowace kasa.

Sanarwar ta ce, duk wani yaki da ta’addanci a Najeriya na gudana ne da nufin kare rayukan fararen hula, tabbatar da hadin kan kasa da kuma kiyaye mutuncin kowane dan kasa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Gwamnatin Tarayya na ci gaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya da tsaro tare da abokan hulda domin tarwatsa gungun ’yan ta’adda, katse hanyoyin samun kudadensu da kuma hana su samun sabbin maboya, tare da karfafa cibiyoyin tsaron gida da kayan leken asiri.

Ma’aikatar ta bayyana cewa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a da sanar da al’umma duk wani ci gaba da aka samu a yaki da ta’addanci ta hanyar shafuka da tashoshin gwamnati da suka dace.

Sanarwar ta fito daga Ma’aikatar Harkokin Waje, Abuja, ranar Juma’a 26 ga Disamba, 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *