Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) murna kan samun damar karɓar baƙuncin Taron Hulɗa da Jama’a na Duniya (World Public Relations Forum, WPRF) na shekarar 2026.
Sanarwar ta zo ne yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, da tawagar sa suka kai wa ministan a ranar 6 ga Maris, 2025.
Ministan ya jaddada muhimmancin taron WPRF, wanda ke haɗa shugabanni da masana a fannin hulɗa da jama’a da sadarwa.
Ya bayyana cewa samun damar karɓar baƙuncin wannan babban taro wata gagarumar nasara ce ga Nijeriya, kasancewar ita ce ƙasar Afirka ta biyu da za ta karɓi baƙuncin taron.
Ya ce: “Wannan babban cigaba ne ga Nijeriya kuma yana da alaƙa da manufofin gwamnatin mu na inganta martabar ƙasar a idon duniya. A daidai lokacin da muke aiwatar da muhimman sauye-sauye da ƙarfafa matsayar mu a duniya, karɓar baƙuncin WPRF wata alama ce cewa duniya tana kallon Nijeriya.
“Gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da nasarar wannan taro.”
Ya kuma bayyana wata muhimmiyar nasara, inda ya ce Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin Cibiyar UNESCO ta Mataki na Biyu kan Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayani (MIL), wadda ita ce irin ta ta farko a Afrika.
Ya ce wannan matakin yana nuna irin girman tasirin da Nijeriya take samu a duniya.
Ya ce: “Hulɗa da jama’a tana da muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa, bunƙasa dimokiraɗiyya, da inganta martabar Nijeriya a duniya.
“Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai tana da ecikakken niyyar yin aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin cimma wannan buri da kuma ba Nijeriya matsayi na jagora a fagen sadarwa na duniya.”
A nasa jawabin, Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, ya yaba wa ministan bisa ƙwazon da yake yi wajen inganta sarrafa bayanai da hulɗa da jama’a a ƙasar.
Ya ce: “Yanzu muna kallon sarrafa bayanai a matsayin hanyar sadarwa ta ɓangarori biyu, wato inda muke karɓar ra’ayoyi daga jama’a don su taimaka mana wajen tsara matakai na gaba.”
Dakta Neliaku ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta karɓi baƙuncin bikin cika shekaru 25 na ƙungiyar Global Alliance a shekarar 2026, wanda hakan zai ƙara tabbatar da matsayin ƙasar a matsayin jagaba a fagen hulɗa da jama’a a duniya.
Bugu da ƙari, ya sanar da ministan manyan shirye-shiryen da NIPR ta tsara na shekarar 2025, wanda suka haɗa da Makon Hulɗa da Jama’a na Nijeriya (NPR Week), Taron Ƙasa na Masu Magana da Yawu, da Taron Ƙasa kan Sarrafa Sunan Nijeriya.
Tawagar shugabannin NIPR ɗin ta haɗa da Mataimakin Shugaba, Farfesa Emmanuel Dandaura, da wasu manyan jami’ai, ciki har da Cif Yomi Badejo-Okusanya, Mohammed Kudu Abubakar, da Cif Uzoma Onyegbadue.