NIJERIYA@65: ‘Yancin iya dogaro da kai shi ne cikakken ‘yanci -Tanimu Yakubu

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Darakta a
Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya, Tanimu Yakubu, ya bayyana cewa duk wani ‘yancin da ƙasa ba za ta iya dogaro da kanta wajen samar da kuɗaɗen bunƙasa tattalin arzikin ta ba, to ba ‘yanci ba ne, holoƙo ne, hadarin kaka.

Yakubu ya bayyana haka a cikin wani saƙon da ya fitar ga ‘yan Nijeriya a ranar zagayowar samun ‘yanci, 1 ga Oktoba, 2025.

A cikin saƙon mai ɗauke da irin yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke gagarimin aikin ciyar da ƙasa gaba ta hanyar tattalin kuɗaɗen ƙasa, Yakubu wanda ƙwararren masanin tattalin arziki ne, ya ce:
“Shekaru sittin da biyar kenan tun bayan da iyayen mu kuma shugabannin mu masu kishi suka ɗaga tuta mai launin kore da fari da kore, ta samun ‘yanci, tare da kafa tarihin rera taken ƙasa mai tabbatar da ƙarshen mulkin mallaka. ‘Yanci ya tabbatar mana mulkin kai a baki. Amma samun ‘yanci ya zama ‘holoƙo hadarin kaka’ idan ba mu da ƙarfin dogaro da kan mu.

“Mun daɗe tsawon lokaci muna dogara da ciwo bashi. Mun riƙa ci da amfani da abubuwan da ba mu ke samar da su ba. Mun riƙa ciwo bashi ido-rufe. Muka zura ido tsawon lokaci ‘yan ƙaƙuduba na yi wa ƙasar mu ‘yankan-aljihu suna kwashe mana arziki.

“A yau kuwa mun kawo ƙarfi, mun farka. Mun fahimci tabbas ba samun ‘yanci kaɗai ne mafita ba. Abin da Nijeriya ke buƙata a yanzu shi ne ‘yancin dogaro da kanta, ta yadda za ta iya riƙe kan ta.”

Da ya koma kan muhimmancin cire tallafin fetur kuwa, Yakubu ya ce: “Abu na farko shi ne an cire tallafin fetur, mun daina lissafin-dawakan-Rano da aikin-baban-giwa, wato bayar da tallafin fetur – tsarin da aka ragargaje tiriliyoyin nairori. An cire tallafin, an toshe hanyar da wasu ‘yan gadangarƙama ke karkatar da Naira tiriliyan huɗu a duk shekara. Waɗannan maƙudan kuɗaɗe a yanzu gwamnati ta karkata su wajen gina titina, makarantu da kuma ayyukan bayar da tallafin sauƙaƙa wa marasa galihu.

“Abu na biyu kuma shi ne mun kawar da tsarin musayar kuɗi mai fuska biyu, wato mai bambancin farashi. Yanzu farashi ɗaya ne. Kasuwa ɗaya ce, kuma gaskiya ɗaya ce.”

Ya ce waɗannan tsare-tsaren bunƙasa tattalin arzikin ƙasa sun zo da tsauri. To amma a gaskiya sun kasance tamkar magani mai ɗaci a baki, kuma mai ingancin warkas da ciwo. Tsare-tsare ne da suka zama na tilas. Su ne mafita ga ƙasar da ta yi hoɓɓasar tsayawa da ƙafafun ta, maimakon ci gaba da dogaro da kayan aro.

“Gwamnatin Tinubu ta bijiro da sauya Dokar Kuɗaɗe (FRA). A yanzu akwai ƙa’idar adadin da za a riƙa yi wa basussuka waigi. A yanzu duk kowane bashin da aka ciwo tilas a ga tasiri da alfanun sa wajen gina makarantu, asibitoci ko gina titina. Lokacin ciwo bashi a yi bushasha ya wuce. Sai dai a ciwo bashi idan ya kama, domin a gina ƙasa,” cewar sa.

Da ya koma kan raba arzikin ƙasa bisa turbar adalci, Yakubu ya ce abu ne mai muhimmanci. “Dalili kenan muka bijiro da Dokar Bada Lamuni ga Ɗalibai, wato ‘Education Loan Fund Act’. Domin a tabbatar cewa talauci bai hana yaro ko guda ɗaya cika burin sa na samun ilmi ba. Za a samar wa kowane fikira da zalaƙa tsanin takawa ya kai gaci. Za a buɗe wa kowa ƙofar samun hasken cimma muradi.

“Kuma dalili kenan muka riƙa matsa-lamba domin Ƙananan Hukumomi su samu ‘yancin cin gashin kuɗaɗen su. Har yanzu ana kan wannan gwadaben, amma lokacin wannan ‘yanci ya zo.

“Tilas daga yanzu za a riƙa gina asibitocin kula da marasa lafiya a wuraren da al’umma suke zaune, ba inda gwamna ke so a riƙa ginawa ba. Tilas a gina makarantu a cikin ƙauyuka, ba sai a manyan garuruwa ko a babban birnin jiha kaɗai ba. Wannan sabon tsari shi ne zai ceto yankunan karkara.

Ya ce ya zama tilas mu kasance muna amfani da kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu ne wajen gina al’umma ta hanyar ta hanyar tsara ingantaccen kasafin kuɗaɗe.

Ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gina titinan jiragen ƙasa, inganta yawan wutar lantarki da ayyukan raya karkara.

Ya ce gwamnati ta tsaurara Asusun Bai Ɗaya na Gwamnatin Tarayya (TSA), an jaddada tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma na GIFMIS. An fasa gayyar ma’aikatan bogi. An ɗinke aljifan da aka huje kuɗaɗen gwamnati na zirarewa. A yanzu ma’aikatu sun san cewa za a iya ƙwaƙulo duk inda wani kobo ya maƙale.

Daga ƙarshe ya ce idan ana kashe kuɗaɗe ta hanyar da ta dace, za a kai ga samun ƙasaita. “Ita kuma ƙasaitar iya dogaro da kai, a nan ne alƙawarin samun ‘yanci na gaskiya yake.” Inji Yakubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *